Dogara ya tura likitocin ido 50 Jihar Bauchi
Shugaban Majalisar Tarayya Honarabul Yakubu Dogara ya tura waxansu qwararrun likitocin kula da lafiyar ido domin gudanar da aikin duba masu fama da cututtukan ido kyauta na mako biyu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Valewa da ke Bauchi.Shugaban ya tura likitocin 50 ne daga Abuja domin su duba waxanda suke da matsala tare […]
Shugaban Majalisar Tarayya Honarabul Yakubu Dogara ya tura waxansu qwararrun likitocin kula da lafiyar ido domin gudanar da aikin duba masu fama da cututtukan ido kyauta na mako biyu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Valewa da ke Bauchi.
Shugaban ya tura likitocin 50 ne daga Abuja domin su duba waxanda suke da matsala tare da ba su gilasan karatu da magunguna kamar yadda wani na hannun damansa Kwamared Iliyasu Zwall ya shaida wa wakilinmu.
Kwamared Iliyasu Ibrahim Zwall wanda Babban Mai Tallafa wa Shugaban Majalisar ne ya shaida wa Aminiya a wajen qaddamar da shirin cewa wannan shiri somin tavi ne za a faxaxa shi zuwa jihohin Arewa maso Gabas.
Ya ce manufar Honarabul Yakubu Dogara ita ce kyautata rayuwar al’umma ba tare da lura da addini ko qabila ba.
Kwamared Zwall ya ce masu matsalar ido daga dukkan qananan hukumomin Jihar Bauchi 20 suna ci gaba da shigowa fadar jiha domin ganawa da likitocin, kuma ana sa ran majiyanta sama da dubu 10 ne za a duba lafiyar idanunsu a asibitin tare da ba su magunguna. “Muna kira ga ’yan siyasar Jihar Bauchi su yi koyi da Barista Dogara domin ya fita zakka a cikin ’yan siyasar Arewa maso Gabas,” inji Zwall.
Da yawa daga cikin waxanda suka amfana da gilasan sun bayyana godiyarsu ga Shugaban Majalisar kan wannan tallafi na ba su magunguna tare da musu tiyata kyauta.