Dogaro da man fetur hadari ne ga Saudiyya – Yarima Talal

daya daga cikin ’ya’yan gidan sarautar Saudiyya kuma daya daga cikin fitattun attajiran duniya Yarima Alwaleed bin Talal ya ce ci gaba da dogaro da kasar ke yi kan arzikin man fetur wani babban hadari na. Yarima Alwaleed bin Talal ya bayyana haka ne bayan faduwar farashin man fetur zuwa kasa da Dala 80 (kimanin […]

Dogaro da man fetur hadari ne ga Saudiyya – Yarima Talal
Dogaro da man fetur hadari ne ga Saudiyya – Yarima Talal

daya daga cikin ’ya’yan gidan sarautar Saudiyya kuma daya daga cikin fitattun attajiran duniya Yarima Alwaleed bin Talal ya ce ci gaba da dogaro da kasar ke yi kan arzikin man fetur wani babban hadari na.

Yarima Alwaleed bin Talal ya bayyana haka ne bayan faduwar farashin man fetur zuwa kasa da Dala 80 (kimanin Naira dubu 13 da 300) kan kowace ganga, lamarin da aka dade ba a ga irinsa ba.
Yarima Alwaleed ya ce faduwar farashin man fetur ya tababtar da shawarar da suka bai wa gwamnatin kasar cewa ta nemi wasu hanyoyin samun kudin shiga maimakon dogaro da man fetur.
Kashi 90 cikin 100 na kudin shigar da Saudiyya ta ke samu suna fitowa ne daga cinikin man fetur.
Yarima Alwaleed ya shaida wa manema labarai cewa wannan matsala ce mai hadari ga tattalin arzikin Saudiyya a nan gaba.
An samu faduwar farashin man fetur ne bayan da kasar Saudiyya ta bayyana rage farashin da take sayarwa ga kasar Amurka.
Tun da farko dai Shugabar Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, Misis Chritine Lagerde ta yi gargadin cewa kasashen Larabawa da kasashen da suke dogaro da man fetur na iya fuskantar matsala a kasafin kudinsu idan aka samu faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya.