Dogaro ga Allah jari
Allah, shi ne wanda ya halicci dukan wata halitta da take bisa bayan kasa ko kuma karkashinta. Haka kuma, Allah Shi ne Ya halicci dukan wata halitta da take cikin sammai karama da babba. Aljannu da mutane, Mala’iku da rauhanai, dukansu da ma wadanda ba su ba, Allah shi ne mai cikakken iko da karfi […]
Allah, shi ne wanda ya halicci dukan wata halitta da take bisa bayan kasa ko kuma karkashinta. Haka kuma, Allah Shi ne Ya halicci dukan wata halitta da take cikin sammai karama da babba. Aljannu da mutane, Mala’iku da rauhanai, dukansu da ma wadanda ba su ba, Allah shi ne mai cikakken iko da karfi akansu. Babu mai ikon yin komai sai tare da yardar Allah da amincewarsa. Babu wata halitta da take mallakar cutarwa ko amfanarwa a hannunta. Allah Shi ne ubangijin kowa da komai, kowa da komai kuma bayin Allah ne.
Janye zancen Boka makaryacin banza! Hatta manyan swalihan bayin Allah, ba su da iko akan amfanar da wani da komai a karkashin ikonsu! Ba su da iko akan cutar da wani da komai. Ba za su iya tabukawa kansu komai ba ballai waninsu, face da cikakkar amincewa da yardar mai kowa mai komai Allah. Sai dai yadda al’amarin yake shi ne, sun rungumi Allah, sun yarda da shi, sun ba shi gaskiya kuma sun bi shi da da’a, to saboda haka, duk abin da suka nema Allah Ya ba su, idan kuma sun nemar ma wani sai Allah Yaba shi.
Da suka raga wa Allah ne, suka girmamar da girmansa, suka dogara gare shi dari bisa dari, shi kuma sai ya girmama su ya darajjanta su. Ya kuma sanya ‘kima da martabarsu a idanuwan al’umma. Har ma ta kai, idan ka labe bayansu, Allah Yakan raga maka domin alfarmarsu. Ai shi ne dalilin da ya sa kake ganin, su kuma ba su tallata girman kowa sai Allah, ba su ganin girman kansu sai dai girman Allah. Allah shi ne gabansu dare da rana. Saboda haka, sai Allah Ya sanya mutane suna ganin girmansu. Kuma suka yarda da su da ayyukansu.
Mu janye zancen bayin Allah magabata, mu dawo akan mutanen da muke rayuwa tare da su a yanzu. Ina nufin masu aikata sabo dare da rana kamar ni, wadanda muke zama tare da su a dandali muyi fira mu she’ke aya. Idan ka kwantar da hankalinka, za ka fahimci cewa, dukan wanda ya mayar da Allah sarki majinginarsa, ya mayar da Allah sarki abin dogaronsa, shi ne mafi sa’ar rayuwa a cikinmu.
Haka abin yake a gefen y’ansiyasa, masu kudi, masu mulki da sauransu. Duk wanda bai bi Allah sau da kafa ba, za ka same shi da dimbin matsaloli a gabansa, kuma ya rasa yadda zai yi da su. Idan ya magance wannan matsalar, nan take sai wata ta sake bullowa. A haka zai ci gaba da rayuwa har zuwa karshen rayuwarsa. Ashe duk yadda kake hangensa kamar a cikin jin dadi, to shi ya san musibar da yake ciki.
Shin dukiya da mulki, duk don me ake nemansu? Domin a samu kwanciyar hankali ne ko? To ga kudin an tara, amma saboda ba a dogara ga wanda ya kamata a dogara da shi ba, sai jin dadi ya buwaya. Bokaye suyi ta wahalar da mutum! Ga shi a cikin suturar mutanen kirki masu hankali, amma sun mayar da shi sha-sha-sha mahaukaci.
Idan ba mahaukaci ba, wa zai saki Allah Ya kama bawa? Iyakar tabewa, ka saki tsayayye wanzajje ka kama wanda shi ma ta kansa yake yi! Shin wai ni in tambaye ka, idan ka dauki boka ko wani a matsayin mai ba ka sa’a ko nasara ko kariya, gaya min, wa ke kule da kai a lokacin da kake kai kadai kana bacci a daki? A daidai wannan lokacin fa, shi ma wancan da kake ganin sai da shi za ka iya yi, yana can yana sharar na shi baccin! Da kai da shi kun shagala. Sai kaka kenan?
Amma idan ka dogara ga Allah ne, to shi Allah rayayye ne kuma wanzajje har abada, don haka ba zai bari a cutar da kai ba. Kuma duk inda ka je yana tare da kai. Duk wata larurar da kake ganin wani zai iya yi maka, to dayan biyu ne, ko ya ro’kar maka Allah tun da shi kadai ne mai bayarwa, ko kuma ya kasance shi ne zai ba ka abin, sai ka roki Allah Ya arzitta ka, ka samu wannan abin ta hanyar wancan mutumen. Wannan ba laifi ba ne.
Amma kam, zancen ‘’idan ba wane ne shugaban ma’aikatar nan ba, ba zan samu abu ba, ko kuma idan ba malam wane ko boka wane ya yi min aiki ba, ba zan samu abu ba, wallahi bata lokaci ne. Domin shi kan shi inda yana da ikon yi wa kansa wani abu, ba za ka tarar da shi a waccan kujerar ba. Kuma idan malami ko Boka na mallakar juya wani al’amari ga hannunsa, to da za ka tarar ya zarce matsayin da yake kai.
Allah Ya jikan marigayi Mammam Shata! Yake cewa a cikin wata wakarsa: In dai tsafi ne, Su fara tsafa ’ya’yansu, Su samo su kawo musu, Ko su ba sa son samun ne sai ni? Da tsohona? Ku tuna fa! Samu ne, gida kudi mota da gidaje! Samu fa, ah haaa!
Wanda ya samar da kai tun babu kai, ya rayar da kai tun ba ka da amfani ga kowa sai dai a amfanar da kai, shi za ka yi wa butulci ka koma neman wani abu ga waninsa? Bawa wanda da kai da shi duk bautar kuke yi? Iyakar ka da mutum ka roke shi alfarmar ya taimaka maka wajen addu’a ga Allah domin biyan bukatarka. Saboda dogaro ga Allah shi ne jari.
Nasir Abbas Babi 08033186727.