Doka kan kalaman tuzura jama’a a kafafen sadarwa
Assalamu alaikum Editan Jaridar Aminiya mai albarka. Don Allah ka ba ni dama in tuna wa ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa abin da ya dace su yi wa doka da farko. Hakika yunkurin ’yan majalisar na samar da doka kan kalaman batanci ko tunzura jama’a a kafafen sadarwa, tamkar barin jaki ne a doki taiki. […]
Assalamu alaikum Editan Jaridar Aminiya mai albarka. Don Allah ka ba ni dama in tuna wa ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa abin da ya dace su yi wa doka da farko. Hakika yunkurin ’yan majalisar na samar da doka kan kalaman batanci ko tunzura jama’a a kafafen sadarwa, tamkar barin jaki ne a doki taiki. Domin kamata ya yi da farko su fara samar da doka mai tsauri a kan masu garkuwa da mutane da masu fyade da masu satar dukiyar kasa kafin kafa dokar da take kokarin tauye ’yancin fadin albarkacin baki ga ’yan kasa, domin wadanan kafafen sadarwa su ne kadai kafar da talaka zai yi kira ga shugabannin su ji.
Daga Aminu Adamu Malam-Madori Jihar Jigawa. 08139041679, 08125319709.
Kira ga Gwamnan Jihar Sakkwato
Assalam Editan Aminiya, barka da warhaka. Allah Ya kara daukaka. Ina son in yi amfani da wannan dama in yi kira ga Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato. Ya kamata Gwamna ya tuna al’ummar Sakkwato mazauna kauyuka suna da alhaki gare ka sun ba ka kuri’arsu ka manta da su, ana ta kashe su kamar kiyashi babu wani matakin kirki da aka dauka kan masu kisansu. Kai ne Gwamna ka kula da hakkin al’ummarka Allah zai tambaye ka ranar da babu ADC, babu CM, babu SA da sauransu. Ka tsaya cikin garinka ka san matsalar jiharka Allah Ya ba ka ikon gyarawa, amin.
Daga Nagoma Guaranty Telor Sabon Titi Ubandoma Road Sakkwato, 08066455877.
Watsi da Arewa: Mu daina
zargin Buhari
Assalam Edita. Don Allah ina so ka ba ni dama domin in fadi ra’ayina a kan abin da ke faruwa a siyasar Arewa. Da yawanmu ’yan Arewa muna zargin Shugaban Kasa Buhari da yin watsi da Arewa wajen ayyukan raya kasa. Abin nake gani ba haka ba ne domin abin da ya sa haka su mutanen Kudu idan aka ba da wani muhimmin aiki to manyansu zuwa suke yi su tsaya a kan sai an yi aikin, amma mu manyanmu ba sa yin haka. Sun fi maida hankali a kan abin da ya shafi kansu da iyalinsu da ’yan uwan matansu, wannan ita ce matsalar Arewa Allah Ya shirye su amin.
Daga Hadi Tsohon Sarki Daura, 08164205067-07015256836.
Kwatar wa ’yan Arewa hakkinsu
Assalam Edita. Don Allah ka mika min gaisuwata da godiyata ga Mai girma Baban Talakawa Sanata Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso game da yadda yake kwatar wa ’yan Arewa hakkinsu a duk inda aka musguna mana musamman a Kudu ko Yammacin kasar nan. Muna ci gaba da addu’a a kan sai ka yi mulkin Najeriya insha Allahu. Gaba dai gaba dai Kwankwasiyya.
Daga Maikudi Ibrahim, Lungun Mabuga Kano. Mazaunin Ajegunle Legas. 09025253392
Tunatarwa ga shugabannin Shanono
Assalam Edita. Ina rokon Aminiya ta mika min tunatarwata ga shugabannin mulki da shugabannin siyasa na Karamar Hukumar Shanono. Talauci da tabarbarewar lamura da koma baya da suka jawo mana, su gyara zai fi kyau.
Daga Tukur Maraya Shanono, 07032442923.
Talakawa mu rungumi kaddara
Salam Edita. Kira ga talakawan Najeriya, mu rungumi kaddara, mu tsaya ga Allah, babu wani shugaba a Najeriya mai gaskiya, in dai ba tausayi.
Daga Abdurrahman Mai Agogo Hadeja 08033836968
Kara wa kayan masarufi haraji
Assalam Edita. Ni fa Aminiya ce aminiyata. Don Allah ku isar min da sakona zuwa ga Shugaba Buhari cewa gaskiya kara wa kayan masarufi haraji ba shi ne mafita ba. Saboda talaka ne kawai zai shiga wahala. Ya kamata ka tuna talaka ne ya kai ka wannan kujera da fatar za a gyara.
Daga Dan’aabe Maizazzau Filin Black Star Neja. 09069405541.
Kira ga masoya Kwankwasiyya
Assalam Edita. Kira ga ’yan uwa masoya Sanata Rabi’u Musa Kwankwanso, ya kamata mu zamo tsintsiya madaurinki daya. Duk abin da ya faru mu bar shi a matsayin ya wuce, mu hari gaba. Allah kuma Ya saka wa jagora Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Ya ba shi lafiya da nisan kwana Allah Ya kara masa tausayin talakawa, amin.
Daga Jibril A. Aliyu Kano, 07034281614.
Ga Gwamna Masari
Assalam Edita, godiya da jinjina ga Gwamna Aminu Masari, Dallatun Katsina bisa ga sake nadA Malam Lawal Buhari a matsayin Shugaban Hukumar Ilimi Bai-Daya ta Jihar Katsina, mun gode Gwamna. Malam Lawal kuma Allah Ya sa alheri, Allah sa ka fi haka, Allah sa APC ta tsaida mana kai takarar Gwamna a zaben 2023 in Allah Ya kai mu, amin.
Daga Amiru Isah Bakori, 07068147933.
Kira ga Gwamnan Jihar Filato
Assalam Aminiya, sakona zuwa ga Gwamnan Jihar Filato, don Allah ya taimaka ya sa baki a kan abin da ke faruwa a tsakanin sarakunan kabilar Tarok. An kama sarakuna an kulle yanzu haka, a yanzu haka dajin yankin ya rude.
Daga Zaliha Abdullahi Fanap Yelwan Shendam, 08133049940.
Tuni ga Gwamnan Jihar Kebbi
Assalam Edita. Don Allah ka ba ni dama in yi kira ga Mai girma Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Atiku Bagudu game da tallafin noman rani da ake bayarwa. Mu mutanen garin Turmin Dutsi, sai dai mu ji a rediyo, don Allah Gwamna a duba a gani.
Daga Jibirin Muhammed Turmin Dutsi Jihar Kebbi, 08065826697.
Zuwa ga Jam’iyyar PDP ta Kasa
Muna kara kira ga uwar Jam’iyyar PDP ta Kasa ta fara kokarin daukar tsatstsauran matakai a kan ’ya’yanta da ake zargi da kayar da ita a zabe, kama daga zabubbukan 2019 zuwa na gwamnoni da aka yi kwanakin baya. Domin na ga tuni tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido da tsohon Shugaban Kasa Dokta Goodluck Jonathan sun fara bayyana kansu. Idan kuwa ba a hukunta su ba, to ta karkashin kasa za su yi wa Jam’iyyar PDP illa. Da fatar za a duba wannan shawara tamu.
Daga Imboka Hadeja 07068066060 da Haruna Danzomo 08068704909.
Kira ga Musulmi da Kiristan Najeriya
Salam Edita. Kira ga Musulmi da Kirista, ya kamata mu zauna lafiya kada mu bari ’yan siyasa su rika hada mu fada. Domin na lura duk lokacin da dan siyasa ya ga bukatarsa ba za ta biya ba, sai ya koma yana hada al’umma fada, ya rika cewa wane ba addininku daya ba shi ne ya yi muku kaza da kaza, kada ku yarda da shi. Su kuma wadanda ba su san inda aka dosa ba sai su dauki makami su je su yi ta kashe wadanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba karshe a kama su a je a tsare su, a kula.
Daga Usman 440 Malumfashi, Bayan NEPA Katsina, 08135815119.
Fatar alheri ga Gwamnan Bauchi
Assalamu alaikum jaridar Aminiya. Ina so in mika sakon godiya ga Mai girma Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed (Kauran Bauchi), bisa namijin kokarin da ya yi na gina Babban Masallacin Juma’a a garin Dogon Jeji, Karamar Hukumar Jama’are. A gaskiya wannan abin farin ciki ne kuma abin a yaba ne. Duk wanda ya taimaki addinin Allah shi ma Allah zai taimake shi. Ina yi maka fatar alheri a kan ayyukkanka na alheri da kake yi. Allah Ya ya saka da alheri, Allah Ya yi jagora, mun gode.
Daga Abdullahi Dibo Jama’are, 08132428869.
Tsaro a Jihar Sakkwato
Salam Edita. Don Allah ku shaida wa Gwamnan Jihar Sakkwato cewa, shi ma ya dauki matakin da gwamnonin Zamfara da Katsina suka dauka wajen sasantawa da ’yan ta’adda. Allah Ya kawo mana karshen barnata dukiya da rayuka da ake yi a Jihar Sakkwato da yankin Arewa gaba daya, amin.
Daga Sulaiman Gidan Dabino Zariya, 08052333864.
Fatar alheri ga ma’aikatan Aminiya
Assalam. Aminiya ina mika sakon gaisuwata gare ku dukkan ma’aikatanku baki daya. Allah Ya kara muku kwazon aiki da basira da mu masu sayen jaridar Aminiya duk mako, Ya ba ku ikon gamawa lafiya, amin.
Daga Balla Maishayi, Karamar Hukumar Kusada Jihar Katsina, 08147872352.
Allah Ka kawo mana karshen
’yan ta’adda
Allah Ka kawo mana karshen ’yan ta’adda masu gwagwarmaya da makamai da sunan addini kamar su Alshabab a Mogadishu fadar gwamnatin Somaliya da sauransu a Saudiyya da ma duniya baki daya.
Daga Abu Yazyd Loko, 08158580946.
Dangantakar Najeriya da
Afirka ta Kudu
Assalam Aminiya. Don Allah ku tuntubi Dokta Sa’id Ahmad Dukawa a kan tarihi da dangantaka a tsakanin Najeriya da kasar Afirka ta Kudu, Allah Ya kara daukaka.
Daga Mai bibiyarku yau da kulum Sani Sulaiman Kwanar Jaba, 08145905398.
A biya ma’aikatan da
suka yi ritaya kudadensu
Assalamu alaikum Editan Aminiya.Ka ba ni dama in mika godiyata da neman taimako ga Gwamnanmu mai adalci Aminu Bello Masari kan ya taimaka ya biya ma’aikatan da suka yi ritaya kudaden sallamarsu. Allah Ya ja zamani mai girma Gwamna amin, 08034628038.
****
Matasa mu tashi mu nemi ilimi
Assalam Edita, ka isar min da sakona ga ‘yan uwana matasa ‘yan darika murika taka tsantsan wajen nunawa Shehunnan Darikarmu soyayya, wallahi wannan daukaka da suka samu sun sameta ne ta hanyar neman ilimi, bai kamata mu zauna da jahilci da sunan soyayya ba har mu rika kai wa ga hallaka ba. Mu tashi mu nemi ilimi.
Daga Shehu Shagari Danja Jahar Katsina 08063844790.
Fatan alheri ga ma’aikatan Media Trust Limited
Salam Edita, ni masoyin wannan jarida ce da bata wuce ni duk mako Ina jinjina maku a bisa kokarin ku na kawo mana labarai masu muhimmanci bisa la’akari da hakan yasa na dau lokaci duk mako wannaa jarida bata wuce ni, kuma duk wanda na karanta sai na sata a durowata na ajiye. Ku huta lafiya.
Daga Abdulkadir Madaro Kurya Jahar Zamfara, 09038657194.
Shari’ar zaben Kano
Salam jaridar AMINIYA mai albarka, ina so ku taimaka min ku isar min da sakona ga kotun data yanke hukuncin zaben Gwamnan Kano Dakta Abdullashi Umar Ganduje da Abba Kabir Yusuf, akan bata yi ma jama’ar Kano dama Najeriya adalci ba duk da gwamnati na ikirarin ita mai adalci ce, amma tana ganin aka yanke hukuncin sanrai ta ki tayi magana. Daga karshe ina yi wa jama’ar Kano jaje da ban hakuri, Allah Ya sakamana amin.
Daga Sulaiman Senior Mowe Jihar Ogun, 09012961055.
Godiya ga Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso
Salam edita, a mika min sakon gaisuwata ga Injiniya Dakta Muhammadu Rabi’u Musa Kwankwaso, akan namijin kokarin tallafawa yaran talakawa zuwa kasar waje karatu da kuma taimakon gina makarantar Islamiya a Ibadan jihar Oyo, ina tayaka fatan alheri.
Daga 08060352323.
Gargadi ga iyaye mata
Assalam Edita, ina muku fatan alheri, ina son naja hankulan iyaye mata gami da maza wadanda basa kishin ‘ya’yansu mata musamman wajan yadda suke barin dama tana wuce su wajan aura musu mazaje, ma’ana wai sai mai tarin dukiya. Wanda hakan bahujjaba bace. In har kun yadda da nagartar mutum kawai ku auramasa. Ku yi musu fatan alheri kawai.
Daga Kabiru Kas Gada Kazaure, 08067707093.
Nadin Kwamishinoni a jihar Jigawa
Nadin Kwamishinoni a jihar Jigawa gara gwamnatin Dakta Sule Lamido. Wai shin ba kwararrun ‘yan boko ne ake nada mana jeka ka dawo?
Daga Sulaiman, 08153685865.
Gyaran kasa da kishin kasa alhakin Gwamnati ne da ‘yan kasa
Salam Edita, gyaran kasa da kishin kasa alhakin Gwamnati ne da kuma ‘yan kasa don haka ya zama dole mu hada karfi wuri guda da gwamnati don kawo ci gaba mai amfani a wannan kasa tamu ba tare da la’akari da bamgaranci ko yare ko kuma kabilanci ko kuma addini ba. Sai don kawai kasarmu ta tsayu akan kafafunta wanda zai kaimu ga samun daukaka da daraja a idanun duniya. Mu dubi manyan kasashe irin su Cana, Jamus da kuma Indiya inda suka yi watsi da duk wani abin da zai kawowa kansu rarrabuwa suka rungumi kasarsu suka zama abin sha’awa a idanun duniya.
Daga Basiru Danbazazzagi 08058591624, 08130616265.
Kasarmu tana bukatar addu’a
Assalam, Edita ina fatan kana lafiya Allah Ya karawa ilimi albarka, don Allah ina so ka ba ni dama nayi kira ga al’ummar kasar mu Najeriya ba muda wata kasa da tafi mana ita, kasarmu tana bukatar addu’a, mu yawaita addu’a akan Allah Ubangiji ya kawo mana zaman lafiya mai dorewa, a maimakon zagin shugabanni da aibantasu, Allah Ya kuma sanya albarka a abinda muka noma amin.
Daga Haladu Ahmadu Chibiyayi Zaki Jihar Bauchi. 08030703952.