Doka ta halasta wa ’yan ƙasa fita zanga-zanga — Peter Obi
Ya rage mana mu saurari masu zanga-zangar nan. Mu tattauna da su mu karɓi kokensu.
Ɗan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar Labour a Zaɓen 2023, Peter Obi ya ce yana goyon bayan masu shirin fita zanga-zangar matsin rayuwa.
Bayan ganawarsa da Gwamna Alex Otti na Jihar Abia a wannan Lahadin, Peter Obi ya yi gargaɗi kan tayar da hankali, inda ya ce ya kamata a gudanar zanga-zanga yadda doka ta tanada.
Aminiya ta ruwaito cewa ana dai ta shirye-shiryen fita zanga-zanga kan tsadar rayuwa a faɗin ƙasar a ranar 1 ga watan Agusta mai kamawa.
Peter Obi ya yi kira ga jami’an tsaro da su bai wa masu zanga-zangar kariya ba tare da wuce gona da iri ba yana mai cewa zanga-zanga ko’ina ta halasta a faɗin duniya.
Tsohon gwamnan na Jihar Anambra ya ce, “Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya halasta zanga-zanga. Amma ina roƙon duk masu shirin fitowa da su yi zanga-zangar cikin lumana yadda doka ta tanadar.
“Babu wanda bai san halin da ake ciki ba a ƙasar nan na matsin rayuwa.
“Abubuwa sun yi matuƙar wahala a ƙasar nan. Ya kamata mu saurari korafe-korafen ’yan Nijeriya,” in ji Obi.
“Idan ana maganar masu ɗaukar nauyin zanga-zangar abubuwa ne masu sauƙin fahimta saboda ba su wuce yunwa da rashin tudun dafawa da matasan ƙasar ke fuskanta ba.
“Saboda haka dole ne a sauri korafe-korafen ’yan Nijeriya.
“Babu wani aibu a zanga-zanga matuƙar an gudanar da ita a bisa tanadin doka.
“Lokacin da nake riƙe da kujerar gwamna na tsawon shekaru an yi min zanga-zanga.
“Saboda haka ya rage mana mu saurari masu zanga-zangar nan. Mu tattauna da su mu karɓi ƙorafinsu da kokensu. Wannan shi ne jagoranci.”
Wannan shi ne karon farko da tsohon gwamnan na Anambra yake bayyana matsayarsa a bainar jama’a kan zangar-zangar da ake shirin gudanarwa.
Sai dai hadimin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan sadarwa, Bayo Onanuga, ya alaƙanta Obi a matsayin ɗaya daga cikin masu ɗaukar nauyin zanga-zangar da cewa magoya bayansa za su kawo hargitsi a ƙasar.
Tuni Obi ya bai wa Mista Onanuga wa’adin sa’o’i 72 ya janye kalamansa ko kuma ya ɗauki matakin shari’a.
Obi ta hannun lauyansa, Alex Ejesieme, ya buƙaci hadimin shugaban ƙasar da ya gaggauta ba da haƙuri tare da wallafa hakan a cikin manyan jaridu huɗu na ƙasar da kuma shafinsa na X (Twitter).
Lauyan Obi ya bayyana zargin da hadimin shugaban ƙasar ya yi a matsayin wata manufa ta ɓata sunan wanda yake wakilta.
Sai dai shi kuma a nasa ɓangaren, har yanzu Onanuga ƙememe ya ƙi bayar da haƙuri duk da barazanar ɗauka matakin shari’a da Obi ɗin ya yi.