Dokar EO6: Ya dace a yi amfani da ita babu son rai
A makon jiya ne Shugaban Basa Muhammadu Buhari ya fara amfani da dokar nan da ta ba shi ikon hanzarta tuhumar duk wani mutum da ake ganin ya mallaki dukiyarsa ta hanyar haram a basar nan, inda ya umarci Hukumar Shigi da Fici da sauran hukumomin tsaro su hana wadansu mutum 50 fita daga basar […]
A makon jiya ne Shugaban Basa Muhammadu Buhari ya fara amfani da dokar nan da ta ba shi ikon hanzarta tuhumar duk wani mutum da ake ganin ya mallaki dukiyarsa ta hanyar haram a basar nan, inda ya umarci Hukumar Shigi da Fici da sauran hukumomin tsaro su hana wadansu mutum 50 fita daga basar nan har sai kotu ta kammala shari’ar da ake yi musu tukun.
Ita dai wannan doka ta Shugaban Basa da ake kiranta da EO6 ta bai wa Shugaban Basa barin iko ne na binciken duk wanda ake zargin ya tara dukiya ta haramtacciyar hanya.
Sai dai kuma umarnin da Shugaba Buhari ya bayar na cewa a hana wadansu mutum 50 fita daga basar nan ya haifar da cece-ku-ce a fadin basar nan, inda wadansu ke ganin hakan da aka yi ya yi daidai, wadansu kuma suna ganin hakan wata hanya ce ta yin bi-ta-da-bulli ga abokan hamayya, musamman da yake yanzu zabe ya barato.
Sai dai kuma da yake barin haske ga manema labarai a fadar gwamnati da ke Abuja, Mai taimaka wa Shugaban Basa ta fuskar hulda da manema labarai Garba Shehu cewa ya yi wannan dokar ba za ta nuna bambancin siyasa ba, an fito da dokar ce domin hanzarta yanke hukunci a kan wadanda ake tuhuma da yin sama-da-fadi da dukiyar gwamnati.
Ya ci gaba da bayanin cewa Shugaba Buhari ya gaji shari’o’in wadannan mutanen ne daga gwamnatocin da suka gabata, amma wadanda ake tuhuma din sai suna amfani da dukiyar da suke da ita wajen kawo cikas ga shari’a, don haka ake so su zauna a cikin basar nan har sai an kammala shari’a, idan dukiyar da ake zarginsu da ita shari’a ta tabbatar tasu ce sai a bar musu, idan kuma an gano cewa ta gwamnati ce sai a bwace.
Ya bara da cewa gwamnati ba ta fitar sunayen mutum 50 da ta bayar da sanarwar cewa ba za a bar su su fita basar nan ba, domin kamar yadda ya bayyana, mutanen sun san kansu, haka kuma mutanen gari sun san su, kuma jami’an tsaro sun san yadda za su aiwatar da dokar.
Amma masu lura da yadda al’amura kan je su dawo na ganin dakatar da manyan mutane guda hamsin daga fita daga basar nan da gwamnati ta yi ana ganin yana da alaba da siyasa, domin me ya sa tuntuni ba a fitar da wannan sanarwar ba sai yanzu da zabe ya gabato?
Haka kuma idan har ana so jama’a su tabbatar babu bi-ta-da-bulli dangane da dokar da kamata ya yi Shugaba Buhari ya fara da wadanda suke kusa da shi, domin ya nuna cewa dokar za ta yi aiki ba sani ba sabo, amma yanzu gani ake kawai za a yi amfani da dokar ce domin takura wa abokan hamayya.
Sannan rashin fitar da sunayen mutum 50 din da aka ce kada su fita ya haifar da shakku a zukatan jama’a, wanda hakan ya sanya suke tunanin lallai wadansu hamshaban mutane da ke adawa da gwamnati ne ake hari, amma ba a so sauran jama’a su gane.
Kamata ya yi a yi wa kowa adalci, kuma adalcin ya zamanto an yi shi a zahiri yadda kowa zai ce lallai ba a nuna son zuciya ba.
Idan gwamnati ta san ba za ta bayyana sunayen mutanen ba da bai kamata ta fitar da sanarwar ba, sai kawai ta sanar da jami’an tsaro, ba tare da sauran mutane sun san halin da ake ciki ba, amma yanzu an bar mutane suna ta yada jita-jita game da sunayen mutanen da aka haramta wa fita.
Wani fitaccen lauya Femi Falana cewa ya yi ba Shugaban Basa ne yake da ikon haramta wa wadannan muranen fita basar nan ba, kotu ce take da wannan ikon, saboda haka kamata ya yi Shugaban Basa ya nemi kotu ta dakatar da mutanen daga fita basar waje, ta haka ne za a tabbatar cewa mulkin dimokuradiyya ake yi ba mulkin kama-karya ba.
A duk lokacin da aka takura wa attajiri guda daya to an takura wa talakawa da yawa ne, domin akwai mutane da dama da ke cin abinci a barbashinsa, shi ya sanya wadansu ke ganin hana irin wadannan mutane walwala zai iya shafar tattalin arziki, saboda haka kamata ya yi a bar kotu ta yi aikinta wajen bincikensu, idan ta ga ya dace ta hana fita shi ke nan, amma takura wa attajiri, takura wa talaka ne. Shi ya sanya Hausawa ke cewa “Mai kudi abokin sarki,” domin yana taimakawa wajen ci gaban basa.
Ya kamata Shugaba Buhari ya yi bobarin ganin cewa ya bambanta gwamnatinsa ta farar hula da gwamnatin soja ta hanyar tuntuba da shawarwari kafin a aiwatar da wasu abubuwa da za su iya haifar wa gwamnatinsa mummunar fahimta.
Ya dace a yi amfani da wannan doka ta EO6 ta hanyar da ta dace, kada a yi amfani da ita yadda za ta haifar da zargi. Domin a halin yanzu saboda rashin bayyana komai a faifai ya sanya abokan hamayya da sauran jama’a suna ta borafi iri-iri.