Dokar gyaran haraji ba za ta cutar da Arewa ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Ƙasa, ta musanta zargin cewa dokar gyaran haraji da ake shirin aiwatarwa za ta cutar da Arewacin Najeriya ko kuma fifita jihohin Legas da Ribas. 

Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce gyaran harajin zai inganta rayuwar ’yan Najeriya, musamman masu rauni, tare da sauƙaƙa tsarin tattara haraji domin tallafa wa kasuwanci.

“Dokokin gyaran haraji ba za su sa Legas ko Ribas su ƙara arziƙi ko su talauta wani yanki ba,” in ji Onanuga.

Ya buƙaci ’yan Najeriya su ƙaurace wa ra’ayoyin da ke ƙoƙarin haifar da rabuwar kai.

Har ila yau, ya bayyana cewa hukumomi kamar TETFUND da NITDA za su ci gaba da samun tallafi ta hanyar kasafin kuɗi.

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, ya yi kira ga shugabannin Arewa su karanci dokar gyaran harajin cikin natsuwa maimakon amfani da jita-jita.

“Ya kamata mu shugabannin Arewa mu mayar da hankali kan ci gaban yankin maimakon ƙabilanci ko bambancin addini,” in ji Dogara yayin wani taron tattaunawa a Abuja.

Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa, kan Gyaran Haraji, Taiwo Oyedele, ya ce manufar dokar ita ce ta taimaka wa jihohi su ƙara samun kuɗaɗe domin dogaro da kansu.