Dokar hana fita: Suna hada kudi don ‘belin’ limaminsu

Mazauna wani kauye da ke Yankin Babban Birnin Tarayya na can suna ta hankoron hada taimako—mai taro, mai sisi—don “belin” limaminsu, kamar yadda suka ce. ’Yan sanda sun kama limamin da wasu mutanen kauyen ne bayan wani artabu da suka yi ranar Juma’a lokacin da al’ummar Damagazam da ke yankin Apo suka bijire wa dokar […]

Dokar hana fita: Suna hada kudi don ‘belin’ limaminsu

Mazauna wani kauye da ke Yankin Babban Birnin Tarayya na can suna ta hankoron hada taimako—mai taro, mai sisi—don “belin” limaminsu, kamar yadda suka ce.

’Yan sanda sun kama limamin da wasu mutanen kauyen ne bayan wani artabu da suka yi ranar Juma’a lokacin da al’ummar Damagazam da ke yankin Apo suka bijire wa dokar hana fita da tarukan jama’a suka yi sallar Juma’a.

Baya ga limamin da ya jagoranci sallar, an kuma kama wasu mutanen kauyen, ciki har da mai-unguwa.

Sai dai wani jagora a yankin ya ce an sako mai-unguwar da safiyar Asabar.

Mazauna yankin dai sun ce matsalar ta auku ne jim kadan bayan fara sallar, lokacin da wasu ‘yan sanda suka fara harbi a sama, sannan suka bukaci da a katse sallar.

Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunanshi ya ce nan take wasu suka gudu, wasu kuma suka tunkari ‘yan sandan da jifa suka kuma lalata motar jami’an tsaron kirar a-kori-kura.

Ya kuma ce sai dai bayan kamar sa’a daya, ‘yan sanda suka sake komawa garin cikin motoci kamar goma.

“Ko da suka dawo kowa ya waste. Sai dai sun fasa gilasan kekuna da wasu suka bari suka tafi arewa a farkon kafa dokar hana zirga-zirga.

“Sun kuma loda babura a motocinsu sun wuce da su”, inji shi.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sanda ta Yankin Babban Birnin Tarayya, DSP Anjuguri Mamza, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai ya musanta zargin cewa ’yan sanda sun fasa gilasan kekuna.

“Wannan ba gaskiya ba ne, ’yan sanda da ke kokarin tabbatar da doka ba za su aikata irin haka ba”, inji shi.

Tun daga karfe 11.00 na daren 30 ga watan Afrilu umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar na hana fita da tarukan jama’a a Yankin Babban Tarayya da nufin hana yaduwar coronavirus ya fara aiki.

Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram 23 A Borno

Fasinjoji sun jikkata yayin da tankar mai ta yi bindiga a Abuja

PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Edo, za ta garzaya kotu

1.5bn kaɗai aka sanya a asusunmu — Tsohon Kwamishinan Sakkwato