Dokar Hana Fita: Tambuwal ya bi sahun Buhari
Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya goyi bayan dokar da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sanya na hana fita daga karfe 8:00 na dare zuwa karfe 6:00 na safe. A ranar Litinin 27 ga Afirilu 2020 ne, shugaba Buhari ya yiwa ’yan Najeriya bayani kan matakan da suke dauka musamman ga wannan annobar […]
Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya goyi bayan dokar da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sanya na hana fita daga karfe 8:00 na dare zuwa karfe 6:00 na safe.
A ranar Litinin 27 ga Afirilu 2020 ne, shugaba Buhari ya yiwa ’yan Najeriya bayani kan matakan da suke dauka musamman ga wannan annobar ta coronavirusta yadda jama’a ke yada cutar ga wasu jama’a.
A jawabin da Tambuwal, ya yi wa jama’ar Sakkwato ya ce bisa ga umarnin da shugaban kasa ya bayar na sanya dokar hana hana fita da daddare a jiharsa daga ranar Litinin 4 ga watan Mayu 2020, har sai yanda hali ya yi.
- Coronavirus ta yi ajalin mutum uku a Sokoto
- Za a samar da cibiyar gwajin coronavirus a Sakkwato
- Buhari ya amince da sassauta doka sannu a hankali
Ya ce dokar ba ta shafi ma’aikata masu aiki na musamman ba, da ma’aikatan gwamnati da suka kai mataki na 13 zuwa sama da dokar zaman gida ba ta shafa ba, amma su sanya takunkumin fuska kafin su tafi wuraren aikinsu.
Akan haka gwamna Tambuwal, ya roki jama’a su ci gaba da daukar matakan yakar wannan cutar, ya kuma roki gwamnatin tarayya ta hannun kwamitin shugaban kasa na yakar cutar da ya tallafawa jihar da kayan aiki domin shawo lamarin kar ya wuce in da ake yanzu.