Dokar hana fita: Yadda rayuwar wasu ta kuntata a Jigawa
Rahotanni sun ce al’ummar garin Kazaure da ke jihar Jigawa sun fada cikin mawuyacin hali bayan da gwamnati ta kafa dokar hana fita wadda ta shafi kowa, har da masu sayar da ruwa a kura. Bayanai dai sun ce a cikin kwaryar garin Kazaure mutanen da ba su da rijiya a gida suna dandana kudarsu. […]
Rahotanni sun ce al’ummar garin Kazaure da ke jihar Jigawa sun fada cikin mawuyacin hali bayan da gwamnati ta kafa dokar hana fita wadda ta shafi kowa, har da masu sayar da ruwa a kura.
Bayanai dai sun ce a cikin kwaryar garin Kazaure mutanen da ba su da rijiya a gida suna dandana kudarsu.
An dai fi samun matsalar ne a unguwannin Tsohon Kafi, da Wajen Gabas, da Matsiga, da Kofar Duzau, da Ganguli, da Sha’iskawa, da Katoge, da Shagari Quarters, da Kantin Gabas da Kantin Yamma da sauransu.
Kamar yadda bayanai suka nuna, ba don ruwan da aka samar a karkashin kulawar wani shiri na Majalisar Dinkin Duniya (SDG’s/SPU) a wasu unguwanni ba, da jama’ar yankunan sun sha matukar wahala.
- Dokar hana fita: Kwalliya na biyan kudin sabulu?
- Coronavirus: ‘Abin da ya sa Jigawa ke kula da wadanda suka kamu’
Wani mazaunin unguwar Ganguli, Malam Isa Usman Ganguli, ya bayyana yadda suka shiga halin ha’ula’i.
“Sakamakon samun wannan cutar mutane sun shiga cikin mawuyacin hali na rashin abinci da matsanancin halin rayuwa.
“Gwamnati ta duba halin da muke ciki duba da yanayin azumi da ake kokarin shiga a ba mu damar yin sayayya saboda mu shirya wa zuwan azumi, kuma a bai wa talakawa damar nikan masara da markaden kayan miya”, inji shi.
Malam Isa ya kuma ce akwai bukatar “a bai wa ’yan-garuwa damar sayar da ruwa ga mabukata saboda alfarmar azumi”.
Shi ma wani mazaunin garin wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce da yake umarnin na gwamnatin jihar Jigawa a kurarren lokaci ta bayar, “lamarin ya sa an samu hauhawar farashin kayan abinci da kashi dari; kuma lamarin ya girgiza rayuwar jama’ar Kazaure”.
Baya ga matsalar rashin ruwa da ta abinci kuma, al’ummar garin na fuskantar rashin wutar lantarki.
Wasu bayanai dai sun nuna cewa tun daga ranar da aka hana fita ba a kawo wutar lantarki ba a garin.
Yunkurin jin ta-bakin shugaban karamar hukumar Kazaure, Jamilu Uwais Zaki, bai yi nasara ba, saboda wayarsa na kashe har zuwa lokacin aiko wannan rahoton.
A cewar daya daga cikin masu ba shi shawara, Honorabul Kwaliya Kazaure, mai yiwuwa shugaban karamar hukumar ya sa wayar caji ne, kuma shi ma tun safe bai gan shi ba.
Amma a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, shugaban karamar hukumar ta Kazaure ya ce Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya ba da umarni a dauki mataki a kan matsalar ruwan da ta addabi jama’ar yankin.
Tun bayan da aka samu wani mutum da aka tabbatar ya kamu da cutar coronavirus a garin ne dai gwamnatin jihar Jigawa ta umarci al’ummar yankin su shiga zaman kulle don hana yaduwarta.