Dokar hana kiwo a Benuwai ce musabbabin yawan gudun hijira a Nasarawa – Gwamnatin Nasarawa

Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa, Mista Silas Ali Agara ya bayyana yawan gudun hijira da al’ummar jihar da na Benuwai ke yi a yanzu daga ainihin garuruwa da kauyukansu zuwa wasu garuruwa daban a jihar don samun mafaka cewa sakamakon dokar hana kiwo da gwamnati da majalisar dokokin Jihar Benuwai ke aiwatarwa a yanzu ne.  Ya […]

Dokar hana kiwo a Benuwai ce musabbabin yawan gudun hijira a Nasarawa – Gwamnatin Nasarawa

Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa, Mista Silas Ali Agara ya bayyana yawan gudun hijira da al’ummar jihar da na Benuwai ke yi a yanzu daga ainihin garuruwa da kauyukansu zuwa wasu garuruwa daban a jihar don samun mafaka cewa sakamakon dokar hana kiwo da gwamnati da majalisar dokokin Jihar Benuwai ke aiwatarwa a yanzu ne. 

Ya bayyana haka ne a jawabinsa a lokacin da ya ziyarci masu gudun hijira dake zaune a makarantan firamaren gwamnati dake garin Doma hedikwatar karamar Hukumar Doma a jihar a karshen makon da ya gabata. Ya bayyana takaici da tausayinsa dangane da halin da ‘yan gudun hijirar suka sami kansu sakamakon aukuwar lamarin da kuma yawansu, inda ya bayyana cewa tuni gwamnatin jihar ta dauki mahimman matakai don tabbatar da ingantaccen tsaro a kauyuka da garuruwa da ake kai hare-hare a jihar musamman wadanda ke iyakokin jihar da makwabtanta Benuwai don kawo karshen kashe-kashen kwata-kwata don bai wa al’ummmar wadannan wurarai damar yin barci da idanuwansu a rufe ba tare da da fargaba ba. 

Ya cigaba da bayyana cewa “kamar yadda kuka sani tuni gwamnatin tarayya ta cika alkawarin da ta yi ta bakin shugaban kasa Muhammadu Buhari na turo ishessun jami’an tsaro musamman sojoji zuwa garuruwa da kauyuka a jihohi shida a kasar nan ciki har da jiharmu ta Nasarawa, inda ake ci gaba da kai hare- hare ana hallaka rayukan al’umma ba gaira ba dalili. Kuma a yanzu sufeto janar na ‘yan sandan kasar nan ya karo jami’an ‘yan sanda zuwa jihar nan. 

Mista Silas Agara ya kara da cewa hakki ne da ya rataya a wuyan gwamnatin jihar ta kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar baki daya saboda haka a cewarsa ya zame mata dole ta tallafawa wadanda lamarin ya shafa, inda ya sanar mu su cewa koda shike babban abin da gwamnati ta sa a gaba shi ne ta tabbatar ta nemi hanyoyin komo da ‘yan gudun hijiran gidajensu na ainihi, amma a cewarsa gwamnatin jihar ta samar musu da kayayyakin agaji don saukake musu zamansu a sansanin kafin ta kammala shirye-shiryen mida su. Daga nan ya jinjinawa karamar hukuma da masarautar Doma karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Doma, Alhaji Ahmadu Aliyu Ogah dangane da tallafi da suke baiwa ‘yan gudun hijiran tunda suka shigo garin na Doma. 

Wakilinmu ya gano kayayyakin agajin da gwamnatin jihar ta baiwa masu gudun hijiran dake Doma, a yayin ziyarar mataimakin gwamnan sun hada da doya da katifu da kwanonin rufin gida da tabarmi da buhunan shinkafa da zanuwa da saurasnu. Idan za a iya tunawa a jawabin gwamnan jihar, Umaru Tanko Almakura a lokacin da ya ziyarci ‘yan gudun hijira dake Obi hedikwatar karamar hukumar Obi a jihar, ya bayyana cewa kimanin ‘yan gudun hijira dubu 25 ne a jihar a yanzu ke zaman hijira a garuruwa daban-daban a jihar. A yanzu dai kawo lokacin nan wakilinmu ya gano kimanin ‘yan gudun hijira 5,000 ne ke zaune a wannan makarantar firamaren gwamnati dake garin Doma.