Dokar hana kiwo za ta kawo matsala a Najeriya – Sale Bayere

Alhaji Sale Bayere shi ne Sakataren kungiyar Ci gaban Al’ummar Fulani ta Najeriya ta Gan Allah, a tattaunawarsa da wakilinmu ya ce kafa dokar hana kiwo da jihohin Ekiti da Benuwai suka yi, za ta kawo matsala a Najeriya:   Me za ka ce game da dokar hana kiwo da wasu jihohi suka yi? Wato […]

Dokar hana kiwo za ta kawo matsala a Najeriya – Sale Bayere

Alhaji Sale Bayere shi ne Sakataren kungiyar Ci gaban Al’ummar Fulani ta Najeriya ta Gan Allah, a tattaunawarsa da wakilinmu ya ce kafa dokar hana kiwo da jihohin Ekiti da Benuwai suka yi, za ta kawo matsala a Najeriya:

 

Me za ka ce game da dokar hana kiwo da wasu jihohi suka yi?

Wato wadannan abubuwa da suke faruwa na kafa dokar hana kiwo, wasu abubuwa ne na bakin ciki. Wannan sana’a ta kiwo da makiyaya suke yi, ba dokar Najeriya ce ta haramta ta ba. Saboda kowanne dan Najeriya yana da ’yancin ya yi walwala kuma ya nemi abin da zai ci a Najeriya. Saboda haka muna mamakin yadda aka fara kafa wannan doka kamar da wasa a Jihar Ekiti. Yanzu kuma ga Jihar Benuwai ita ma ta kafa dokar, ita ma Jihar Taraba tana maganar cewa wannan doka za ta fara aiki a jihar a watan Janairun badi.  Muna ganin wannan abu wata karamar wuta ce da ta taso wadda idan ba a yi hankali ba za ta ci Najeriya baki daya. Saboda a ce makiyaya wadanda sun kai sama da mutum miliyan 20 an hana su harkar kiwo a Najeriya ana kawo misali da wasu kasashe da suka ci gaba na Turai. Muna son mu gaya wa duniya cewa wadannan kasashe da suka ci gaba ba su da makiyaya na gargajiya. Don haka ba sa yin kiwo na gargajiya. Suna yin kiwo na zamani ne.

Mu kuma makiyayanmu a nan Najeriya da kasashen Afirka tun lokacin da Annabi Musa (SAW) ya fara kiwo har zuwa yau, makiyayanmu suna tashi daga wannan wuri suna bin ciyawa da ruwa idan ruwan ya yi yawa su tashi su koma can. Don haka makiyayanmu har sukan tafi yankunan Yarbawa da Ibo da Neja-Delta su zauna. Saboda Najeriya kasa ce da kowane dan Najeriya yake da ’yancin ya je ya zauna a duk inda ya ga dama. Saboda haka wannan mataki da wasu jihohin Najeriya suka fara dauka na kafa dokar hana kiwo a jihohinsu yana ba mu mamaki kwarai da gaske. 

Wannan ruwa na kogin Benuwai ba na Jihar Taraba ko Benuwai ba ne. Ruwan kogi, ruwa ne daga Allah, wanda ya taso tun daga kasashen Kamaru ya gangaro ta duwatsun Mambila har zuwa teku da ke Legas. Saboda haka babu wani mutum da zai ce albarkatun ciyawa da ruwa da ke wadannan wurare na wani ne. 

Kuma muna gaya wa gwamnatin Jihar Benuwai cewa wannan doka da suka kafa ya kamata a sake duba ta. Saboda mun fahimci cewa a cikin wannan doka, akwai tozartawa da kabilanci da bambancin addini da cin mutuncin makiyaya. Mun fahimci an kafa dokar ce domin a musguna wa mutanenmu, saboda kabilanci da kyamar addini da kiyayya da hassadar da ake yi wa mutanenmu. Saboda haka muna kira ga Gwamnan Jihar Benuwai ya dubi matsalar da ke tattare da wannan doka. 

Shi kuma Gwamnan Jihar Taraba muna son ya sani cewa doka ce ta kafa ofishin Gwamna kuma doka ce ta ba shi ayyukan da yake yi. Bayan faruwar rikicin yankin Mambila da aka yi a kwanakin baya, mun bi dukan matakan da suka kamata a dauka mun dauka. Mun bai wa mutanenmu hakuri kan kisan gillar da aka yi musu daga nan muka dauki mataki na kai gwamnatin jihar a gaban Babbar Kotun Jihar, muka yi karar Gwamnan kan cewa ba ya da hurumin kafa wannan doka a kundin tsarin mulkin Najeriya. Bayan haka mun sake kai karar gwamnatin Jihar Benuwai da Gwamnatin Tarayya a gaban Kotun Afiika ta Yamma kan kafa dokar hana kiwo a Jihar Benuwai da kuma abin da aka yi wa mutanenmu A yankin Mambila. Haka mun sake kai karar Gwamnatin Jihar Taraba da Gwamnatin Tarayya a gaban Kotun Duniya kan kisan gillar da aka yi wa mutanenmu a Mambila. Ba mu ga dalilin da zai sanya Gwamnan Jihar Taraba ya dauki doka a hannunsa ya kafa dokar ba, domin mun kai kara gaban kotuna uku kan wannan al’amari. 

Wadanne illoli ne kake ganin kafa dokar zai kawo a Najeriya?

Kamar yadda muke gaya wa mutane lokacin da aka fara kafa dokar a Jihar Ekiti mun ce idan ba a yi wani abu a kan wannan lamari ba, wata jiha ma za ta ce za ta yi, domin akwai jihohi da yawa da suke gaba da makiyaya, saboda an dauko addini da kabilanci a sanya a maganar makiyaya a Najeriya. Amma abin bakin ciki gwamnatocin Najeriya ba su iya yin komai ba kan wadannan abubuwa da ake yi wa makiyaya.

 Idan ka ce za ka kori makiyaya a duk wuraren da suke da ciyawa da ruwa, Jihar Nasarawa ba za ta iya daukarsu ba. Jihar Neja ba za ta iya daukarsu ba, Jihar Kwara ba za ta iya daukarsu ba, Jihar Kogi ba za ta iya daukarsu ba, Jihar Filato ba za ta iya daukarsu ba, Jihar Bauchi ba za ta iya daukarsu ba, Jigawa ko Borno ba za su iya daukarsu ba. Abin da muke fada shi ne a yi mana adalci, matsalar wannan doka a fili take. Mu ba mu da wata sana’a sai wannan sana’a ta kiwo, ita ce iyayenmu da kakanninmu suka yi, da ita muke ci da ita muke sha, don haka duk wanda ya hana mu wannan sana’a ya tsokano bala’i.  

Wane kira ne kake da shi zuwa ga gwamnati game da hanyoyin da za a bi, a warware wannan matsala?

Abin da muke so Gwamnatin Tarayya ta yi shi ne, a fitar da Fulani makiyaya daga Ma’aikatar Gona ta Tarayya, domin wannan ma’aikata masifa ce a wurin Fulani makiyaya. Saboda an ce wannan ma’aikata ce ta manoma da makiyaya amma yanzu wannan ma’aikata ta zama ma’aikatar manoma kadai. Mu abin da muka sani kasar nan mu ne miya manoma ne tuwo. Ka ga idan babu miya babu yadda za a ci tuwo, saboda haka ya kamata a yi mana adalci a wannan ma’aikata ta hanyar ware mana kasonmu a duk kasafin kudin da za a yi. Don haka muna so Gwamnatin Tarayya ta tsaya wajen ganin an yi mana hukumar kula da makiyaya ta Najeriya, wadda za ta kula da harkokin kiwo a Najeriya.