Dokar haramta luwadi da madigo: Ko hukuncin daurin shekaru 14 ya yi daidai?

A kwanakin baya ne Shugaban kasa ya rattaba hannu ga dokar haramta luwadi da madigo a Najeriya, inda dokar ta tanadi daurin shekaru 14 ga duk wanda aka kama da laifi. Abin tambaya a nan shi ne, ko wa’adin ya yi daidai, ya yi kadan ko ya yi yawa? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mutane kamar […]

Dokar haramta luwadi da madigo: Ko hukuncin daurin shekaru 14 ya yi daidai?
Dokar haramta luwadi da madigo: Ko hukuncin daurin shekaru 14 ya yi daidai?

A kwanakin baya ne Shugaban kasa ya rattaba hannu ga dokar haramta luwadi da madigo a Najeriya, inda dokar ta tanadi daurin shekaru 14 ga duk wanda aka kama da laifi. Abin tambaya a nan shi ne, ko wa’adin ya yi daidai, ya yi kadan ko ya yi yawa? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mutane kamar haka:

Wa’adin ya yi daidai – Abdulkarim Umar

Abdulkarimu Umar: “A ra’ayina game da wannan hukunci na daurin shekaru 14 da Gwamnatnin Tarayya ta yanke wa masu wannan mummunan aiki ya yi daidai, idan da wani abu da za a kara a kan wannan hukunci to gwamnati ta haramta musu abin da ya danganci aiki na mulkin kasa kowane iri. Domin ina ganin ko ba komai wannan hukuncin zai zama babban darasi ga sauran mutane su kuma za su koyi hankali tare da gane babban laifin da suka aikata.