Dokar haramta luwadi da madigo: Ko hukuncin daurin shekaru 14 ya yi daidai? 1

A kwanakin baya ne Shugaban kasa ya rattaba hannu ga dokar haramta luwadi da madigo a Najeriya, inda dokar ta tanadi daurin shekaru 14 ga duk wanda aka kama da laifi. Abin tambaya a nan shi ne, ko wa’adin ya yi daidai, ya yi kadan ko ya yi yawa? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mutane kamar […]

Dokar haramta luwadi da madigo: Ko hukuncin daurin shekaru 14 ya yi daidai? 1
Dokar haramta luwadi da madigo: Ko hukuncin daurin shekaru 14 ya yi daidai? 1

A kwanakin baya ne Shugaban kasa ya rattaba hannu ga dokar haramta luwadi da madigo a Najeriya, inda dokar ta tanadi daurin shekaru 14 ga duk wanda aka kama da laifi. Abin tambaya a nan shi ne, ko wa’adin ya yi daidai, ya yi kadan ko ya yi yawa? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mutane kamar haka:

Hukuncin  ya yi daidai – Barista Rabi’u

Barista Rabi’u Yusuf: “Gaskiyar Magana, wannan hukumci na daurin shekaru 14 da aka tanadar wa da ’yan luwadi a Najeriya ya yi daidai, don haka ina goyon baya da wannan hukumci dari bisa dari. Saboda dukkan addinan da muke bi a kasar nan, na Musulunci da Kiristanci, sun haramta want ton al’amari na aikata luwadi domin mummunan laifi ne. An nuna cewa saboda munin wannan laifi sai da Ubangiji Ya azabtar da wata al’umma kan aikata wannan laifi, don nuna ishara ga sauran al’ummar duniya.