Dokar haramta luwadi da madigo: Ko hukuncin daurin shekaru 14 ya yi daidai? 2

A kwanakin baya ne Shugaban kasa ya rattaba hannu ga dokar haramta luwadi da madigo a Najeriya, inda dokar ta tanadi daurin shekaru 14 ga duk wanda aka kama da laifi. Abin tambaya a nan shi ne, ko wa’adin ya yi daidai, ya yi kadan ko ya yi yawa? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mutane kamar […]

Dokar haramta luwadi da madigo: Ko hukuncin daurin shekaru 14 ya yi daidai? 2
Dokar haramta luwadi da madigo: Ko hukuncin daurin shekaru 14 ya yi daidai? 2

A kwanakin baya ne Shugaban kasa ya rattaba hannu ga dokar haramta luwadi da madigo a Najeriya, inda dokar ta tanadi daurin shekaru 14 ga duk wanda aka kama da laifi. Abin tambaya a nan shi ne, ko wa’adin ya yi daidai, ya yi kadan ko ya yi yawa? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mutane kamar haka:

Wa’adin ya yi kadan – Alhaji Ahmadu

Alhaji Ahmadu Adamu: “Da farko dai ina goyon bayan dokar saboda haka wannan hukuncin na shekara 14 ya yi amma kuma da so samu ne, duk wadanda aka kama da irin wannan babban laifin ko da hukuncin kisa ne gwamnatin ta yanke musu ya yi daidai, domin babu masifar da ta wuce gaban aikata luwadi ga al’ummar kasa.