Dokar haramta luwadi da madigo: Ko hukuncin daurin shekaru 14 ya yi daidai? 3

A kwanakin baya ne Shugaban kasa ya rattaba hannu ga dokar haramta luwadi da madigo a Najeriya, inda dokar ta tanadi daurin shekaru 14 ga duk wanda aka kama da laifi. Abin tambaya a nan shi ne, ko wa’adin ya yi daidai, ya yi kadan ko ya yi yawa? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mutane kamar […]

Dokar haramta luwadi da madigo: Ko hukuncin daurin shekaru 14 ya yi daidai? 3
Dokar haramta luwadi da madigo: Ko hukuncin daurin shekaru 14 ya yi daidai? 3

A kwanakin baya ne Shugaban kasa ya rattaba hannu ga dokar haramta luwadi da madigo a Najeriya, inda dokar ta tanadi daurin shekaru 14 ga duk wanda aka kama da laifi. Abin tambaya a nan shi ne, ko wa’adin ya yi daidai, ya yi kadan ko ya yi yawa? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mutane kamar haka:

Hukumcin bai yi tsanani ba -Alkali Ishak Jos
Alkali Ishak danjuma Jos: “Wannan hukumci na daurin shekaru 14 da aka tanadar wa duk wanda ya aikata laifin luwadi a kasar nan, an yi ne a matsayi na mutumtaka. Amma idan muka dubi wannan laifi a bisa ka’idar addinin da muke bi a kasar nan na Musulunci da Kiristanci, babu wanda ya amince da aikata wannan laifi. A shari’ar Musulunci, duk wanda ya aikata wannan laifi za a kashe shi ne amma kamar yadda Shugaban kasa ya amince da want ton hukumci na daurin shekaru 14 ga duk wanda ya aikata wannan laifi, wannan an yi ne a matsayin mutumtaka.