Dokar haramta luwadi da madigo: Ko hukuncin daurin shekaru 14 ya yi daidai? 4
A kwanakin baya ne Shugaban kasa ya rattaba hannu ga dokar haramta luwadi da madigo a Najeriya, inda dokar ta tanadi daurin shekaru 14 ga duk wanda aka kama da laifi. Abin tambaya a nan shi ne, ko wa’adin ya yi daidai, ya yi kadan ko ya yi yawa? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mutane kamar […]
A kwanakin baya ne Shugaban kasa ya rattaba hannu ga dokar haramta luwadi da madigo a Najeriya, inda dokar ta tanadi daurin shekaru 14 ga duk wanda aka kama da laifi. Abin tambaya a nan shi ne, ko wa’adin ya yi daidai, ya yi kadan ko ya yi yawa? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mutane kamar haka:
Hukuncin kisa ya kamata – Hajiya Maimuna
Hajiya Maimuna Mai Naman Kaza: “Tir, Allah wadaran mai wannan dabi’a, don me Allah Ya yi mace da namiji kuma ya ce su zauna tare amma kuma wasu su ce wai sai auren jinsi guda za su yi? Wannan wace irin masifa ce? Abin da muke ji can wata duniya, yau ga shi ya zo mana kuma ai hukuncin shekaru 14 ya yi kadan. Idan da za a bi shawarata ce, da hukuncin kisa ya kamata a zartar kan wadannan masu wannan mummunar dabi’ar.”