Dokar haramta luwadi da madigo: Ko hukuncin daurin shekaru 14 ya yi daidai? 5

A kwanakin baya ne Shugaban kasa ya rattaba hannu ga dokar haramta luwadi da madigo a Najeriya, inda dokar ta tanadi daurin shekaru 14 ga duk wanda aka kama da laifi. Abin tambaya a nan shi ne, ko wa’adin ya yi daidai, ya yi kadan ko ya yi yawa? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mutane kamar […]

Dokar haramta luwadi da madigo: Ko hukuncin daurin shekaru 14 ya yi daidai? 5
Dokar haramta luwadi da madigo: Ko hukuncin daurin shekaru 14 ya yi daidai? 5

A kwanakin baya ne Shugaban kasa ya rattaba hannu ga dokar haramta luwadi da madigo a Najeriya, inda dokar ta tanadi daurin shekaru 14 ga duk wanda aka kama da laifi. Abin tambaya a nan shi ne, ko wa’adin ya yi daidai, ya yi kadan ko ya yi yawa? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mutane kamar haka:

Bayan dauri a kara wani hukuncin – dahiru Haladu

dahiru M. Haladu: “Na farko dai Allah Ya ce bai halicci mutane da aljanu ba sai don su bauta maSa. Saboda haka ina ganin wannan hukuncin ya yi kadan idan muka yi la’akari da abin da Alkur’ani ya fada a game da hukuncin masu aikata wannan sabon. Don haka ko mutum bai sani ba, Ubangiji Ya hana namiji ya sadu da dan uwansa namiji, kamar yadda malamai suke fada a kodayaushe. Ni a ganina, a kyale yawan shekaru 14 na dauri amma kuma a kara da wani hukuncin mai tsanani ko dai bulala ko wani abin, ta yadda zai kara tsorata masu aikata wannan laifin, kada su yi ko ma marmarin aikatawa.”