Dokar haramta luwadi da madigo: Ko hukuncin daurin shekaru 14 ya yi daidai? 6

A kwanakin baya ne Shugaban kasa ya rattaba hannu ga dokar haramta luwadi da madigo a Najeriya, inda dokar ta tanadi daurin shekaru 14 ga duk wanda aka kama da laifi. Abin tambaya a nan shi ne, ko wa’adin ya yi daidai, ya yi kadan ko ya yi yawa? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mutane kamar […]

Dokar haramta luwadi da madigo: Ko hukuncin daurin shekaru 14 ya yi daidai? 6
Dokar haramta luwadi da madigo: Ko hukuncin daurin shekaru 14 ya yi daidai? 6

A kwanakin baya ne Shugaban kasa ya rattaba hannu ga dokar haramta luwadi da madigo a Najeriya, inda dokar ta tanadi daurin shekaru 14 ga duk wanda aka kama da laifi. Abin tambaya a nan shi ne, ko wa’adin ya yi daidai, ya yi kadan ko ya yi yawa? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mutane kamar haka:

Hukuncin ya gaza – Garba danla

Garba danla: “Gaskiya ni a ganina wannan hukuncin ya yi kadan kwarai da gaske, domin ko idan ka dubi Najeriya, kashi 98 mabiya addinan nan ne guda biyu; ko dai Musulunci ko kuma Kirista kuma duka wadannan addinai biyu ba wanda ya yarda da wannan mummunar dabi’a. Saboda haka ni ina ganin hukuncin daurin shekaru 14 sun yi kadan. Idan ma da hali, ni gani nake yi kamata ya yi a gaggauta kara shekarun domin shekarun gidan yari sun sha bamban da na waje. Kuma  ni ina ganin cewa ko wadanda ma ba su da addini ba su yarda da wannan abu ba, ke nan wasu ne ke neman kawo mana bakuwar al’ada da karfi da yaji, don haka idan zai yiwu to a kara wannan hukuncin.”