Dokar haramta luwadi da madigo: Ko hukuncin daurin shekaru 14 ya yi daidai? 7

A kwanakin baya ne Shugaban kasa ya rattaba hannu ga dokar haramta luwadi da madigo a Najeriya, inda dokar ta tanadi daurin shekaru 14 ga duk wanda aka kama da laifi. Abin tambaya a nan shi ne, ko wa’adin ya yi daidai, ya yi kadan ko ya yi yawa? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mutane kamar […]

Dokar haramta luwadi da madigo: Ko hukuncin daurin shekaru 14 ya yi daidai? 7
Dokar haramta luwadi da madigo: Ko hukuncin daurin shekaru 14 ya yi daidai? 7

A kwanakin baya ne Shugaban kasa ya rattaba hannu ga dokar haramta luwadi da madigo a Najeriya, inda dokar ta tanadi daurin shekaru 14 ga duk wanda aka kama da laifi. Abin tambaya a nan shi ne, ko wa’adin ya yi daidai, ya yi kadan ko ya yi yawa? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin mutane kamar haka:

Hukuncin ya wadatar – Usman Umar

Usman Umar Gundu: “Ni a nawa ra’ayin, hukuncin daurin shekaru 14 ga wanda aka kama da laifin saduwa da mutum dan jinsinsa kamar mace da mace ko namiji da namiji, hakan ya yi daidai. Ina ganin tun da dauri a gidan fursuna abu ne mai tsanani da takurawa ko da kuwa na dan karamin lokaci ne, balle har a tsare mutum tsawon shekaru 14. Yin hakan zai shafi rayuwar mutumin ta yadda zai yi asarar shekaru da dama yana tsare. Haka nan kuma ina ganin idan aka hukunta mutum da wannan daurin to ba ma sai an ce masa kada ya sake aikatawa ba, domin ya isa a ce ya koyi darasin da shi da kansa zai rika yi wa wadansu gargadin kada su aikata wannan laifin, a saboda wahalar rayuwar da ya shiga.”