Dokar haramta nuna wariya ga nakasassu
A makon jiya ne labari mai dadin ji ya shiga kunnuwan al’ummar Najeriya, wato lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannun tabbatar da dokar haramta nuna wa nakasassu wariya ta 2018. An yi ta musayar yawu a tsakanin Majalisar Dokoki ta Kasa da Bangaren Zartarwa, inda Shugaban Kasa ya nuna cewa ba a turo masa […]
A makon jiya ne labari mai dadin ji ya shiga kunnuwan al’ummar Najeriya, wato lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannun tabbatar da dokar haramta nuna wa nakasassu wariya ta 2018. An yi ta musayar yawu a tsakanin Majalisar Dokoki ta Kasa da Bangaren Zartarwa, inda Shugaban Kasa ya nuna cewa ba a turo masa dokar ba, ita kuma majalisa ta ce ta sanya mata hannu kuma ta tura ta tun 2018. Yanzu dai gardandamin sun kare, tunda an kai ga tabbatar da ita.
Wannan doka dai tun shekara 18 da suka gabata ake kokuwa a kanta, sai ga shi sai a bana ne Majalisa ta 8 ta amince da ita. A ranar 28 ga Maris, 2018 aka mika kudirin dokar ga Majalisar Dokoki ta Kasa inda ita kuma taa gama aikinta ta mika ga Shuagban Kasa a cikin watan Disamban da ya gabata. Mai taimaka wa Shugaban Kasa kan Harkokin Majalisar Dattawa, Sanata Ita Enang ya ce: “Dokar ta haramta a nuna wa nakasassu kowace irin wariya ko wulakantarwa, wanda kuma ya yi haka za a ci shi tarar Naira miliyan daya, idan hukuma ce ko kamfani ko ma’aikata, idan kuma mutum ne ya aikata haka, za a ci shi tarar Naira dubu 100 ko daurin wata shida a kaso ko kuma a hada biyun gaba daya.”
Hakkokin da suka wajaba ga nakasassu sun hada da ilimi, kiwon lafiya, kulawa ta musamman a wuraren zama ko wuraren aiki ko kuma lokacin faruwar wani hadari, dole a ba su kulawa ta musamman fiye da masu lafiya. Haka kuma dokar ta ba nakasassun da aka nuna wa wariya damar su shigar da kara ko korafi a kotu domin neman hakkinsu.
An haramta a nuna wa nakasassu wariya a tashoshin mota ko jirgin ruwa ko na kasa. Haka kuma lallai ne kamfanonin sadarwa su samar wa nakasassu hanyoyin biyan bukatunsu na sadarwa na musamman. Haka kuma, gine-ginen ma’aikatun gwamnati ko na masu zaman kansu, wajibi ne su samar da wurare na musamman domin amfanin nakasassu cikin sauki.
Kamar yadda dokar ta tanada, za a kama jami’in gwamnati mai kula da bayar da izinin gini da laifi, idan har ya ba da izinin wani gini da ya saba wa kula da hakkokin nakasassu. Bisa ga karya wannan doka, za a ci tarar wannan jami’i Naira miliyan daya ko daurin shekara biyu a gidan kaso ko a hada masa biyun gaba daya.
Nakasasshe na nufin mutumin da ya samu tawaya ko ta ji ko gani ko tabin hankali. Haka kuma za a iya nuna wa mutum wariya ne idan aka yi amfani da wata dama da ta saba wa shi nakasasshen, aka hana shi hakkinsa ta wannan yanayin. Misali, a lokacin da ake watsa bayani ga al’umma ta talabijin, ya kamata a ce an samu mai bayyanawa da alamar hannu, domin kurame su fahimta, rashin samar da mai fassara da hannu, kamar nuna wariya ne ga kurame.
Dokar dai ta bukaci duk wata ma’ikata ko cibiya ta gwamnati ko mai zaman kanta ta ware kashi biyar cikin dari na guraben aiki domin nakasassu. Haka kuma ta bukaci a kafa hukuma ta musamman mai kula da al’amuran nakasassu, inda za a nada mata Babban Sakatare, wanda kuma dole ya kasance daga cikin nakasassun. An diba wa dokar tsawon shekara biyar ta fuskar aiwatarwa ta bangaren gine-gine da wuraren taruwar al’umma, yadda za su samar da hanyoyin biyan bukatun nakasassu, har ma da guragun da ke amfani da keken guragu.
Mu a nan, muna yaba wa Gwamnatin Tarayya da ta sanya wa dokar nan hannu, musaman ganin cewa kusan shekara 20 ana ta faman nema mata gurbi amma sai yanzu. Don haka ya kamata a yi duik mai yiwuwa wajen ganin cewa ana amfani da dokar sau da kafa. Ya kamata a shiga gangamin wayar da kan al’umma domin a fahimci dokar sosai. Gwamnati ta yi kokari wajen samar wa nakasassu makarantu na musamman, kamar na makafi da kurame domin su samu ingantaccen ilimi. Haka kuma ya kamata Kungiyar Kwadago ta sanya ido sosai ta bangaren daukar nakasassu aiki, kamar yadda dokar ta sama musu damar haka.