Dokar Kulle: El-Rufa’i ya jinjina wa Musulmin Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i ya jinjina wa Musulmin jihar Kaduna bisa juriya da hakurinsu a lokacin azumin watan Ramadan wanda aka yi cikin dokar kulle a jihar. El-rufa’i ya shaida haka ne a sakon gaisuwar sallahd ya aike wa al’ummar Musulmi wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter. Malam Nasir @elrufai has congratulated […]
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i ya jinjina wa Musulmin jihar Kaduna bisa juriya da hakurinsu a lokacin azumin watan Ramadan wanda aka yi cikin dokar kulle a jihar.
El-rufa’i ya shaida haka ne a sakon gaisuwar sallahd ya aike wa al’ummar Musulmi wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Malam Nasir @elrufai has congratulated the Muslim community on the successful completion of Ramadan in unusually challenging circumstances. He commended the patience and understanding displayed in observing the obligations of faith under conditions of quarantine.
— Governor of Kaduna (@GovKaduna) May 24, 2020
“Gwamna Nasir El-Rufai na taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin Ramadan a cikin wannan mawuyacin yanayi.
“Ya yaba da juriya da fahimtar da suka nuna yayin gudanar da ayyukan ibada a cikin yanayin dokar hana fita,” inji sanarwa.
A jihar Kaduna an gudanar da azumin watan Ramadan da sallar idi a cikin dokar kulle da gwamna Nasir El-Rufa’i ya ayyana a kokarinsa na kare yaduwar annobar coronavirus.