Dokar kulle: El-Rufa’i ya nemi afuwar jama’a

Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya nemi afuwar jama’a bisa matakan kulle da ya sanya a jihar a kokarin gwamnatinsa na dakile yaduwar coronavirus. El-Rufa’i ya ce matakan sun zama wajibi ne don kare al’umma daga cutar. Wani hoton bidiyo da gwamnatin Kaduna ta wallafa a shafinta na Twitter ya nuna El-Rufai da uwargidansa, Aisha […]

Dokar kulle: El-Rufa’i ya nemi afuwar jama’a

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Elrufa’i lokacin da yake sintirin tabbatar da dokar kullen da ya kafa tana aiki a kwanakin baya

Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya nemi afuwar jama’a bisa matakan kulle da ya sanya a jihar a kokarin gwamnatinsa na dakile yaduwar coronavirus.

El-Rufa’i ya ce matakan sun zama wajibi ne don kare al’umma daga cutar.

Wani hoton bidiyo da gwamnatin Kaduna ta wallafa a shafinta na Twitter ya nuna El-Rufai da uwargidansa, Aisha Garba El-Rufa’i, suna zaune a kan kujera suna gode wa al’ummar Kaduna da suka bi umarnin dokar zaman gida.

Gwamna El-Rufa’i ya ce “a  matsayina na gwamnanku, ina neman afuwarku, amma hakan (dokar kulle) ta zama wajibi domin daƙile yaduwar wannan annoba”.

Ya kara da cewa a matsayinsa na ganau ba jiyau ba, COVID-19 cuta ce mai hadarin gaske da za ta iya halaka mutum, kuma hanya guda da za a kawo karshenta shi ne a hana zirga-zirgar jama’a.

Haka zalika uwargidan gwamnan ta mika godiyarta ga ma’aikatan kiwon lafiya bisa jajircewarsu  wurin yaki da cutar, ta kuma jaddada kira ga mutane da su ci gaba da yin biyayya ga dokar kullen.

Tun a makon farko da El-Rufai ya hana fita a Kaduna, gwamnati ta kama wasu malamai biyu da laifin karya dokar bayan sun jagoranci sallar Juma’a a masallatansu.

Elrufa’i ne dai gwamna na  farko da  ya dauki matakin kulle jiharsa a cikin gwamnonin arewacin Najeriya, kana shi ne mutum na farko da aka tabbatar ya kamu da coronavirus a jihar Kaduna.

Zuwa daren 16 ga watan Mayu, alkaluman da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta wallafa sun nuna cewa jihar Kaduna na da mutum 138 da suka kamu da cutar COVID-19.