Dokar kulle: Tsananin ciwo ya sa sun cire hakori da filaya
Rahotanni sun ce daya daga cikin mutum hudu na wadansu masu ciwon hakori a Birtaniya sun yi wa kansu maganin ciwon hakoran ta hanyar fizge su da filaya. Wani bincike da Gidauniyar Oral Health Foundation da hadin gwiwar Colgate suka gudanar wanda ya yi nazarin matasa dubu biyu, ya gano kashi 24 cikin 100 sun […]
Rahotanni sun ce daya daga cikin mutum hudu na wadansu masu ciwon hakori a Birtaniya sun yi wa kansu maganin ciwon hakoran ta hanyar fizge su da filaya.
Wani bincike da Gidauniyar Oral Health Foundation da hadin gwiwar Colgate suka gudanar wanda ya yi nazarin matasa dubu biyu, ya gano kashi 24 cikin 100 sun yi yunkurin magance ciwon hakoransu a gida yayin da aka kakaba dokar kulle sanadiyyar bullar cutar Coronavirus.
- Kwastam ta kama kasusuwan zaki da hauren giwa na N1bn
- APC ta roki jami’an tsaro su binciko wanda suka kashe shugabanta
- El-Rufai ga Gumi: Ba za mu yi sulhu da ’yan bindiga ba
Kashi 55 cikin 100 kuma sun yi watsi da kula da lafiyar hakoransu yayin da ake fama da dokar kullen.
Wani rahoto da aka daddale ya nuna kashi 19 cikin 100 ko mutum daya cikin biyar ba sa iya wanke hakoransu sau biyu a rana kamar yadda masana kiwon lafiya suka bukata.
Nazarin ya samar da wani haske kan yadda wasu kasashe ke daukar matakan kiwon lafiyar hakoransu.
Wani rahoto na Healthwatch England ya nuna yadda aka yi ta samun korafe-korafen kan ciwon hakora a lokacin dokar kullen COVID-19.
A watan Oktoban bara, wani magidanci mai suna Chris Savage mai shekara 42 kuma mahaifin ’ya’ya uku da ke garin Southsea a birnin Portsmouth na kasar Birtaniya, ya sha kwalaben giya takwas kafin daga bisani ya cire hakoransa biyu a dakinsa, bayan ya gaza yin rajista da likitan hakora.
Chris Savage wanda lebura ne ya dade yana fama da ciwo a muka-mukinsa, hakan ya sa ya yanke shawarar cire hakoran.
Chris ya bayyana wa kafar labarai ta The News cewa, “Da farko na yi tunanin fita daga cikin hayyacina saboda ba na sha’awar yin haka.
“Ba wanda zai so ya yi amfani da filaya a fuskarsa, saboda ba a yi ta don a amfani a fuska ko magance wani ciwo ba.
“Na yi amfani da filayar a hakorina, da na sake yi sai na ji zafi, sai da na ji zafi har na dakata na tsawon minti biyar,” inji shi.
A wani labarin kuma wani mai suna Billy Taylor daga wani yankin kasuwanci na Administer a Karamar Hukumar Devon a Birtaniya, shi ma ya cire hakorinsa da filaya bayan matsanancin ciwo da yake yi masa.
Mista Billy ya yi kokarin kiran lambar neman agaji amma sai likitan ya ce masa, ba zai iya ba shi taimako ba sai dai idan yana fuskantar matsalar shakar numfashi ce.
Billy ya bayyana wa majiyar The Sun cewa, “Tsananin ciwon hakorin ya sa fuskata ta kumbura ga tsananin ciwo a muka-muki.”
Binciken da aka gudanar kwanan nan ya gano cewa, matsalar tana faruwa ne a bangaren kiwon lafiyar hakora, sakamakon cin abinci marasa inganci da shaye-shaye.
Sai kuma cin kayan kwadayi kafin a sanya dokar kulle sannan kashi 11 cikin 100 suna shan giya.
Shugaban Gidauniyar, Nigel Carter ya yi gargadin cewa, a guji yin jinya a gida ga wadanda ba a horar don yin haka ba, kuma yin magani ga wanda bai samu horo ba na da hadari ga lafiyar mutum.