Dokar Majalisa kan takara matasa aka yi wa gata – Abdulhadi Kila

Wani jagoran kungiyoyin matasa a harkokin siyasa, Alhaji Abdulhadi Kila Katsina ya ce, dokar da ‘yan majalisa suka kawo babu wanda ta fi yi wa dadi irinsu matasa, domin su ne kashin bayan cigaban al’umma. Matsahin ya ce tun da aka samu ‘yancin kai da kuma fara siyasa a kasar nan ba a taba ba […]

Dokar Majalisa kan takara matasa aka yi wa gata – Abdulhadi Kila

Wani jagoran kungiyoyin matasa a harkokin siyasa, Alhaji Abdulhadi Kila Katsina ya ce, dokar da ‘yan majalisa suka kawo babu wanda ta fi yi wa dadi irinsu matasa, domin su ne kashin bayan cigaban al’umma.

Matsahin ya ce tun da aka samu ‘yancin kai da kuma fara siyasa a kasar nan ba a taba ba matasa wata dama a siyasance ta a dama da su irin wannan lokacin ba. 

“Tabbas zamu iya cewa mu matasa mun fara ganin canji a wannan lokaci. Har’ila yau, irin wannan damar ce da muka rasa tun farko ya sa aka mayar da mu tamkar karnukan farauta. Kamar yadda na sha gayawa matasan mu ne ke kirkiro abu a siyasance kuma mu ne zamu ci gaba da wahala akan renon abin, amma kuma a karshe sai dai mu ga ana yi.” 

“Dan karamin misalin da zan bada anan akan irin rawar da muke takawa a wajen ci gaban siyasa shi ne, ni din nan na jagoranci kungiyoyin siyasa da dama anan Jahar Katsina duk kuwa nunawa matasan da nike yi akan cewa kada su dauki siyasa a matsayin sana’a domin ba za su tafi tare ba. Duk da ina da karancin shekaru a wancan lokacin amma na fara taka rawar siyasa tun daga 1999, amma ban fara fice ba sai a 2001, inda na fara jagorantar kungiyoyi na siyasa anan jahata har zuwa yau. Kuma jama’a ne ke jawo ni su ba ni shugabanci da zarar an buga kugen siyasar,” a cewarsa. 

Ya ci gaba da cewa, “Haka kuma a irin siyasar da muke takawa a kungiyance ita ce, zamu dauki dan takarar da muke ganin zai kawo mana cigaba”. Sai dai matashin dan siyasar ya ce, da zarar dan takararsu ya ci zabe to shike nan sun rabu da shi, domin mu babbar bukatarsu ita ce in an kafa gwamnati a samarwa matasa abin yi.

Misalin irin kungiyoyin da na fara jagoranta sun hada da ta magoya bayan Sule Musa ‘Yar’adua wadda a karshe muka mayar da ita kungiyar matasa magoya bayan ‘Yar’adua a cikin shekara ta 2001 wadda kuma wannan kungiya ce muka taho da ita har acikin 2007 wanda anan ma mun dauke ta domin tafiya a harkoki na PDP, amma a karshe saboda muna kanana a harkar sai wasu daga sama suka kwace mana ita kungiyar suka mayar da ita kungiyar  ‘Yar’adua, inda suka yi amfani da wannan suna a wajen takarar Umaru na shugaban kasa, aka bar mu anan kasa wajen takarar ita PDP a matakin jaha. 

“To a shekarar 2011 sai muka sake dauko wata kungiyar amma a wannan karon ba karkashin PDP ba a karkashin jam’iyar CPC a wancan lokacin, inda muka dauko matasan ‘yan takara domin mu tallata su wato Yakubu Lado da ya tsaya takarar gwamna a jahar Katsina tare da mataimakinsa Abdu Soja. Ita ma wannan kungiyar matasan ta magoya bayan Yakubu Ladon ni ne aka ba shugabancinta kuma daga wurina ne a wannan lokacin aka fara ganin fastocin tallar dan takara tare da manufofinsa.” 

Ya cigaba da cewa “A can baya lokacin da ake cewa Shema Gwamnan dole a wajena aka fara ganin fastar shi bayan da aka ce ba Masari za ayi ba. A 2015 nan ma mun yi shawarar bin Aminu Bello Masari a kungiyance, nan ma ni ne shugaban kungiyar ta magoya baya,” in ji shi.

Da Aminiya ta so jin ta bakin shi Abdulhadi akan yadda ake barin matasa a baya a duk lokacin da wata jam’iya ta kafa gwamnati, sai ya ce e, hakan na faruwa wanda kuma shi a nashi ganin laifin na matasan ne ba ‘yan siyasa ba, domin su matasan su ne suka nuna hanyar da har ake barin su baya. Kila ya ce, maimakon matasan nan su tsaya akan manufofin kafa kungiyoyinsu tare da tabbatar da cewa an sama masu abin yi kamar yadda ake magana da su da farko, sai kawai su shigo da wani abin daban ga wadanda suka yi wa wahala har suka kafa gwamnati.