Dokar Masana`antun Man Fetur(PIB): yanzu kuma ya ragewa `yan Majalisar Dattawa su dage
Daga bakin Sanata Bukar Abba Ibrahim (ANPP Yobe), na fara jin irin illoli da munakisar da aka kudunduna a cikin dokar Masana`antun Man fetur da ake wa lakabi da PIB, a lokacin da ya shigo wani shirin gidan Radiyon Freedom mai suna Barka da Hantsi da nike gabatarwa, a watan Janairun bana. Daftarin dokar, wadda […]
Daga bakin Sanata Bukar Abba Ibrahim (ANPP Yobe), na fara jin irin illoli da munakisar da aka kudunduna a cikin dokar Masana`antun Man fetur da ake wa lakabi da PIB, a lokacin da ya shigo wani shirin gidan Radiyon Freedom mai suna Barka da Hantsi da nike gabatarwa, a watan Janairun bana. Daftarin dokar, wadda marigayi shugaban kasa Alhaji Umaru Musa `Yar`aduwa ya fara gabatar wa Majalisar Dattawa, amma kuma bayan rasuwarsa, zuwan shugaba Goodluck Jonathan akan karagar mulki ya yi kiranye ga daftarin dokar inda ya yi mata kwaskwarima, sannan ya sake mayar da ita ga Majalisar.
A wancan shiri na Barka da Hantsi,Sanata Bukar Abba cewa ya yi su `yan Majalisar Dattawa sun ki kula wancan daftarin doka ne saboba wai ta kunshi yadda ake son a sake kwashe arzikin man fetur din kasar nan a baiwa al`ummomin yankunan da ake hako man fetur din, baya ga kashi 13 cikin 100, da yanzu ake ba jihohin da ake hako man fetur din daga yankunansu. Ya kuma fadi cewa daftarin dokar ya tanadi dimbin iko ga ofishin Ministar man fetur cikin aiwatar da dokar da sarrafa wadancan kudade.
Ilai kuwa, sai ga wadancan zarge-zarge na Sanata Bukar Ibrahim sun bayyana a ranaikun Alhamis da Juma`ar makon jiya, a lokacin da hadin guiwar Kwamitocin Majalisar Dattawa na harkokin man fetur dana shari`a, a wani zaman sauraren ra`ayoyin masu ruwa da tsaki akan hada-hadar man fetur da sauran jama`ar kasa ya shirya a Abuja ya kara fito da wadancan zarge-zarge na Sanata Bukar Abba karara, kamar yadda dukkan wadanda suka bayyana a wajen sauraren ra`ayoyin jama`ar kama daga jami`an Hukumomin gwamnatin tarayya da na jihohi, ba wanda ya goyi bayan tanade-tanaden daftarin, illa Ministar Albarkatun man fetur Misis Diezani Allison Madueke, wadda daga ofishinta daftarin dokar PIB din ta fito.
Alal misali, a gabatarsa, shugaban Hukumar rabon arzikin kasar nan da ake wa lakabi da RMAFC, Mista Elias Mbam, da Kwamishina a Hukumar Alhaji Umar Abba Gana ya wakilta, cewa ya yi samar da kafa asusun don al`ummomin yankunan da ake hako man fetur daga yankunansu, ya ci karo da tanadin rabon arzkin kasar nan na a rabashi tsakanin hukumomin gwamnatoci uku wato gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi dana Majalisun kananan Hukumomi, wanda kuma karya tanadi tsarin mulki ne. Ya kuma fadi cewa abinda ake so a yi wajen kafa asusun da zai tanadi kashe 10 cikin 100, na ribar da Kamfanonin da suke hako man fetur su bayar don tallafawa al`ummomin, tuni tanadin kashi 13 cikin 100, da ake bayarwa, wanda kuma ke da tanadi a cikin tsarin mulki, yake kulawa da wannan batu.
Shugaban Hukumar ta RMAFC, ya kuma fadi cewa bayan kashi 13, akwai kuma Hukumomi irinsu Ma`aikatar Yankin Neja Delta da Hukumar Raya yankin Neja Delta, wadanda duk ya ce Hukumomi ne da gwamnatin tarayya ke tanadarwa da makudan kudade don ganin kyautatuwar yankin da mutanensa. Wani batu kuma da Mista Mbam ya yi tsokaci akan wannan daftarin doka ta masana`antun man fetur, shi ne irin dimbin ikon da aka tanadarwa Mnistar Albrkarun man fetur, tanade-tanaden da ka iya raunana karfin ikon da Kamfanonin da za a samar a karkashin dokar.
Ita ma Hukumar tabbatar da ayyukan gwamnati da hukumominta cikin gaskiya da adalci, wato NEITI, a cikin ta ta gudummuwar akan daftarin dokar, shugabanta Mista Ledum Mitee ya gabatar, cewa ta yi tsarin daftarin dokar bai fayyace dalla-dalla ba irin yadda za a rika raba kudaden da Kamfanoni masu hakon man fetur din zasu rinka biya ba a cikin asusun, bare kuma akan wace bukata za a kashesu ga al`ummomin. Ya ce maimakon yin hakan, daftarin dokar Ministan ma`aikatar ya tanadarwa, kuma babu wani kayyadanjen lokaci na ta yi hakan.
Wakilan gwamnonin jihohi biyu da suka bayyan gaban kwamitin sauraren ba`asin kafa dokar, wato na jihar Neja, wanda kuma shine Kwamishinan shari`a Alhaji Abdullahi Bawa, cewa ya yi dimbin ikon da daftarin dokar ya tanadarwa da Ministar ko kadan bai dace ba, don a fadarsa dokar zata shafi dukkan kasa baki daya. Wani hamzari da gwamnan na Neja ya bayar shi ne kara samar da kashi 10 cikin 100, ga al`ummomin da ake hako man daga yankinsu (kudaden da ya ce zasu rinka kai Naira biliyan 176, a shekara), zai sanya kason naso a cikin arzkin kasa ya koma kashi 23 cikin 100, al`amarin da ya ce kokusa na zai taimakawa zamantakewar al`ummomin kasar nan ba. Shi ma wakilin gwamnan jihar Kaduna, wanda shi ma Kwashinan shari`a ne na jihar, Mista Jonathan Kish Adamu, kamar sun hada baki da sauran jami`an gwamnatin taraya da gwamnan jihar Neja, don kuwa koke-koken sukar daftarin dokar da wadancan jami`ai suka yi shima su ya gabatar a madadin gwamnatin jihar Kaduna.
Su ma kansu Kamfanoni masu hada-hadar hako man fetur a kasar nan, ta bakin shugaban kungiyarsu Mista Mark Ward, cewa sukai ko kusa tanade-tanaden da daftarin dokar suka kunsa ba za su taimaka wa harkokin zuba jari ta bangaren man fetur ba a kasar nan. Yana mai jaddada cewa ko kusa ba ta irin yadda zaka yi ka zuba jari akan harkar man fetur ka ci riba, abinda ka iya sa masu zuba jari a fannin su rinka ja da baya wajen zuwa kasar nan don zuba jari a fannin man fetur.
Ita kuwa Ministar Al`amurran man fetur, wadda kuma ma`aiktarta ta gabatar da daftarin dokar, Misis Deizani Allison Madueke, cewa ta yi bai kamata a sa siyasa ko kuma a mayar da daftarin dokar tamfar wata doka ta kashin kanta, tana mai cewa sun sha wahalar gaske, wajen ganin sun samar da daftarin dokar, ta kara da cewa ko kusa dokar ba ta kai ta kasashe irinsu kasar Birtaniya ko Norway ko Malaysia ba, akan tanade-tanade iko da gunadanwar. Ra`ayinta ne cewa masu hasashen ta jibgawa kanta dimbin iko cikin dokar, lalle su rinka la`akari da cewa dokar zata kai shekaru shidda zuwa bakwai kafin kankamarta, wanda ya zuwa wancan lokaci ita ko shugaban kasa Jonatthan, ba wanda ke kan karagar mulki.
Da irin wanna zube ban kwarya da aka yi, kasan cewa akwai lauje a cikin nadi, don haka bai kamata ba a ce `yan Majalisar Dattawa da dukkan wadanda alhakain tabbatar da wannan daftarin doka yake wuyansu, a ce sun zuba idanu dokar ta kai labari. Ya kamata `yan Majalisin Dokoki na kasa da dukkan masu fada a ji su tuna da cewa da irin wannan barazana mutanen kudu maso yamma suka samu gaba muka dauki mulkin kasarnan a shekarar 1999, muka mika masu a bagas, yanzu ga irin halin da kasr take ciki, Irinwaccan barazana `yan yankin Neja Delta suka yi suka sanya aka tanadar masu kashi 13 cikin 100, na arzikin man fetur din kasar a cikin kundin tsarin mulki da kafa masu Hukumomi na musamman don raya yankunansu, yanzu kuma sun dawo suna neman karin kasha 10, bayan wasu shekaru kuma ba wanda zai ce ga yadda za su ce a yi. Don haka yanzu ya kamata a ce an ki.