Dokar sai mai digiri kadai zai tsaya takarar mukami a Najeriya ta dace?
A yayin tattaunawa a Zauren Taron Makomar kasa, wasu membobi sun ba da shawarar cewa ya kamata a kafa dokar da za ta tabbatar da cewa duk mai son tsayawa takarar zaben kowane mukami, tun daga Kansila har zuwa Shugaban kasa, dole sai ya mallaki shaidar Digiri ko Babbar Difiloma. Abin tambaya a nan shi […]
A yayin tattaunawa a Zauren Taron Makomar kasa, wasu membobi sun ba da shawarar cewa ya kamata a kafa dokar da za ta tabbatar da cewa duk mai son tsayawa takarar zaben kowane mukami, tun daga Kansila har zuwa Shugaban kasa, dole sai ya mallaki shaidar Digiri ko Babbar Difiloma. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan dokar ta dace kuwa ko ba ta dace ba? Ga ra’ayoyin jama’a, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:
Abdulrazak Adefemi: “A gaskiya bisa la’akari da cewa komai sai da ilimi, shi ya sa nake goyon bayan wannan matakin. Kuma idan kudirin ya tabbata, zai taimaka wajen samun shugabanni masu ilimi sosai. Kodayake dabi’un dan Adam ba sun ta’allaka ne kan zurfi koyawan karatunsa ba, amma ilimi mai zurfi na da matukar amfani ga kowane mahaluki, musamman ma ga jagoran al’umma.”