Dokar sai mai digiri kadai zai tsaya takarar mukami a Najeriya ta dace? 1
A yayin tattaunawa a Zauren Taron Makomar kasa, wasu membobi sun ba da shawarar cewa ya kamata a kafa dokar da za ta tabbatar da cewa duk mai son tsayawa takarar zaben kowane mukami, tun daga Kansila har zuwa Shugaban kasa, dole sai ya mallaki shaidar Digiri ko Babbar Difiloma. Abin tambaya a nan shi […]
A yayin tattaunawa a Zauren Taron Makomar kasa, wasu membobi sun ba da shawarar cewa ya kamata a kafa dokar da za ta tabbatar da cewa duk mai son tsayawa takarar zaben kowane mukami, tun daga Kansila har zuwa Shugaban kasa, dole sai ya mallaki shaidar Digiri ko Babbar Difiloma. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan dokar ta dace kuwa ko ba ta dace ba? Ga ra’ayoyin jama’a, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:
Matakin bai kamata ba – Abubakar Isa
Abubakar Isa Musa: “A fahimta ta, wannan ba mataki ba ne mai kyau saboda a gaskiya ba adalci ba ne a ce sai mai shaidar digiri ne kawai zai shugabancin jama’a. A sani na, shugabanci ana duba mutumin kirki ne, wanda yake da halaye kyawawa. Misali, ’yan majalisar dattijan kasar Birtaniya mutane ne da ba zabensu ake ba, nada su jama’ar yankin da suke wakilta ke yi bias la’akari da halayensu kyawawa da gogewar su amma ba zurfin karatu ba. Haka kuma ya kamata a ce mun yi a kasar nan, ba dole sai wanda ke rike da takardar shaidar digiri ba ne ya dace da zama shugaba nagari.”