Dokar sai mai digiri kadai zai tsaya takarar mukami a Najeriya ta dace? 2

A yayin tattaunawa a Zauren Taron Makomar kasa, wasu membobi sun ba da shawarar cewa ya kamata a kafa dokar da za ta tabbatar da cewa duk mai son tsayawa takarar zaben kowane mukami, tun daga Kansila har zuwa Shugaban kasa, dole sai ya mallaki shaidar Digiri ko Babbar Difiloma. Abin tambaya a nan shi […]

Dokar sai mai digiri kadai zai tsaya takarar mukami a Najeriya ta dace? 2
Dokar sai mai digiri kadai zai tsaya takarar mukami a Najeriya ta dace? 2

A yayin tattaunawa a Zauren Taron Makomar kasa, wasu membobi sun ba da shawarar cewa ya kamata a kafa dokar da za ta tabbatar da cewa duk mai son tsayawa takarar zaben kowane mukami, tun daga Kansila har zuwa Shugaban kasa, dole sai ya mallaki shaidar Digiri ko Babbar Difiloma. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan dokar ta dace kuwa ko ba ta dace ba? Ga ra’ayoyin jama’a, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:

Dokar ta dace amma da gyara – Muhammad Auwal

Muhammad Auwal: “A gaskiya ya kamata a yi la’akari da wasu abubuwa kafin ma a rika zartar da kowace irin doka, musamman ma a mukaman siyasa. Ina laifi a ware cewa duk wani mai son rike mukamin siyasa tun daga kan Shugaban karamar hukuma zuwa mataki na Shugaban kasa a ce sai mai digiri amma a ce Kansila mukaminsa ma sai haka ba a yi la’akari da wasu abubuwa ba, musamman masu shaidar difiloma da takardar malanta ta NCE.
Kamata ya yi su yi doka mafi kankantar takardar shaida ta kasance karamar difiloma ko shaidar malanta ta NCE, alabashi sauran mukaman ire-iren su mukamin Shugaban kasa na Majalisun Tarayya, su sai su kasance sai mai digiri.