Dokar sai mai digiri kadai zai tsaya takarar mukami a Najeriya ta dace? 3

A yayin tattaunawa a Zauren Taron Makomar kasa, wasu membobi sun ba da shawarar cewa ya kamata a kafa dokar da za ta tabbatar da cewa duk mai son tsayawa takarar zaben kowane mukami, tun daga Kansila har zuwa Shugaban kasa, dole sai ya mallaki shaidar Digiri ko Babbar Difiloma. Abin tambaya a nan shi […]

Dokar sai mai digiri kadai zai tsaya takarar mukami a Najeriya ta dace? 3
Dokar sai mai digiri kadai zai tsaya takarar mukami a Najeriya ta dace? 3

A yayin tattaunawa a Zauren Taron Makomar kasa, wasu membobi sun ba da shawarar cewa ya kamata a kafa dokar da za ta tabbatar da cewa duk mai son tsayawa takarar zaben kowane mukami, tun daga Kansila har zuwa Shugaban kasa, dole sai ya mallaki shaidar Digiri ko Babbar Difiloma. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan dokar ta dace kuwa ko ba ta dace ba? Ga ra’ayoyin jama’a, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:

Dokar ba ta dace ba– Ibahim Wadatau

Ibrahim Wadatau Jamalu: “Wannan doka da kwamitin nan ke neman ya kafa ko ya kakaba wa ’yan Najeriya gaskiya za ta yi tsauri, musamman ga mutanenmu. Yanzu a ce mukamin Kansila ma sai mai digiri, to gaskiya ba a yi wa mutane adalci ba. Ina ma a ce su kafa dokar ta fara daga masu neman mukamin Shugaban karamar hukuma zuwa majalisar jiha ko ta tarayya? Idan da wadannan ne aka ce sai ma mai digiri biyu, babu laifi amma Kansila a ce sai kana da digiri babu adalci a cikin dokar. Idan an yi haka, ni a nawa ra’ayi gaskiya wannan doka a kasar nan ba na jin za ta yi wani tasiri.”