Dokar sai mai digiri kadai zai tsaya takarar mukami a Najeriya ta dace? 4
A yayin tattaunawa a Zauren Taron Makomar kasa, wasu membobi sun ba da shawarar cewa ya kamata a kafa dokar da za ta tabbatar da cewa duk mai son tsayawa takarar zaben kowane mukami, tun daga Kansila har zuwa Shugaban kasa, dole sai ya mallaki shaidar Digiri ko Babbar Difiloma. Abin tambaya a nan shi […]
A yayin tattaunawa a Zauren Taron Makomar kasa, wasu membobi sun ba da shawarar cewa ya kamata a kafa dokar da za ta tabbatar da cewa duk mai son tsayawa takarar zaben kowane mukami, tun daga Kansila har zuwa Shugaban kasa, dole sai ya mallaki shaidar Digiri ko Babbar Difiloma. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan dokar ta dace kuwa ko ba ta dace ba? Ga ra’ayoyin jama’a, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:
Babu dacewa a dokar – Ali Manzo
Ali Manzo Sarkin Doya: “Ni a ganina, wannan tsarin na cewa sai mutum yana da takardar shaidar digiri kafin ya tsaya takara bai dace ba, domin ai siyasa ba ta bukatar zurfin karatun boko. A siyasa, idan mutum zai yi takara, abin da ake bukata kawai takardar shaidar karatu na sakandare. Saboda idan aka ce sai mutum yana da digiri kafin ya tsaya takara daga Kansila zuwa Shugaban kasa, to ai daraja ko martabar kujerun ai ba daya ba ne. Kujerar Kansila ba ta kai ta Shugaban karamar hukuma ba, haka Shugaban karamar hukuma bai kai dan majalisar jiha ba, haka dan majalisar jiha bai kai dan majalisar tarayya ba; shi ma dan majalisar tarayya bai kai Sanata ba Sanata kuma bai kai Gwamna ba, haka Gwamna shi ma bai kai Shugaban kasa ba, to don mene ne za a ce sai mutum yana da digiri kafin ya tsaya takara kowanne iri? Ina ba da shawara ga su wakilan da suke taron makomar kasar da cewa su sake tunani, wannan tsari da suke bullo da shi.”