Dokar sai mai digiri kadai zai tsaya takarar mukami a Najeriya ta dace? 5

A yayin tattaunawa a Zauren Taron Makomar kasa, wasu membobi sun ba da shawarar cewa ya kamata a kafa dokar da za ta tabbatar da cewa duk mai son tsayawa takarar zaben kowane mukami, tun daga Kansila har zuwa Shugaban kasa, dole sai ya mallaki shaidar Digiri ko Babbar Difiloma. Abin tambaya a nan shi […]

Dokar sai mai digiri kadai zai tsaya takarar mukami a Najeriya ta dace? 5
Dokar sai mai digiri kadai zai tsaya takarar mukami a Najeriya ta dace? 5

A yayin tattaunawa a Zauren Taron Makomar kasa, wasu membobi sun ba da shawarar cewa ya kamata a kafa dokar da za ta tabbatar da cewa duk mai son tsayawa takarar zaben kowane mukami, tun daga Kansila har zuwa Shugaban kasa, dole sai ya mallaki shaidar Digiri ko Babbar Difiloma. Abin tambaya a nan shi ne, shin wannan dokar ta dace kuwa ko ba ta dace ba? Ga ra’ayoyin jama’a, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:

Matakin ya dace – Samuel Anya

Samuel Anya: “Ni a nawa ra’ayin, batun sai mutum yana da takardar shaidar digiri sannan zai tsaya takara, hakan ya dace saboda rashin ilimi yakan sa shugaba ya zama bai san ’yanci al’ummarsa ba. Duk wanda zai tsaya takara muddin yana da ilimi, babu yadda zai yi ya bari ya ga an take hakkin al’ummarsa ya bari saboda ya san abin da yake yi. Idan ka ga shugaba koda Kansila din ne bai yin shugabanci yadda ya dace, rashin ilimi mai zurfi ne domin babu yadda za a yi a ce yau za ka shugabanci jama’a masu yawa amma ba ka da basira ko wadataccen ilimin da zai ba ka dama ka yi mu’amula da mutane yadda ya kamata. Muddin shugaba yana da ilimi, ba zai taba bari ya ga an karkatar da hakkin al’ummar da yake wa shuganci, ya bari ba.”