Dokar ta-baci: Gwamnati da gangan take yi –Khalifa Hassan Yusuf

Wakilin Aminiya ya tattauna da daya daga cikin dattawan wannan yanki, wanda aka dama da shi a harkokin siyasar kasar nan a jiya da yau. Wannan bawan Allah shi  ya gaji marigayi jagoran ‘yan NEPU da PRP, Malam Aminu Kano, wato Khalifa Alhaji Hassan Yusuf, inda ya yi tsokaci kan dokar ta-baci da shugaban kasa […]

Dokar ta-baci: Gwamnati da gangan take yi –Khalifa Hassan Yusuf
Dokar ta-baci: Gwamnati da gangan take yi –Khalifa Hassan Yusuf

Wakilin Aminiya ya tattauna da daya daga cikin dattawan wannan yanki, wanda aka dama da shi a harkokin siyasar kasar nan a jiya da yau.

Wannan bawan Allah shi  ya gaji marigayi jagoran ‘yan NEPU da PRP, Malam Aminu Kano, wato Khalifa Alhaji Hassan Yusuf, inda ya yi tsokaci kan dokar ta-baci da shugaban kasa ya saka  a jihohin nan uku. Ga yadda hirar ta kasance.

Aminiya: A matsayinka na tsohon dan siyasa a kasar nan, wanda ya taba tsayawa takarar shugaban kasa, ya kake ganin dokar ta-baci da aka sanya a jihohin wannan yanki uku?
 Khalifa: Wannan dokar ta-baci abu ne sananne , don ina daya daga cikin ’yan kwamitin da suka rubuta tsarin mulkin kasar nan da ya tanadi dokar, har kuma sojoji suka zo suka amince da ita. Kuma irin wannan doka dama doka ce da ta bada dama ga shugaban kasa ya kafa ta a duk lokacin da ya ga al’amura sun tabarbare, wato in babu tsaro a kasa, ko ana yaki ko in yunwa ta fada wa kasa da makancin hakan.
Dokar ta-baci da shugaban kasar ya kafa a jahohinmu uku ba ya rasa nasaba da tabarbarewar harkokin tsaro da bangaren jahohin ke fuskanta, duk da cewar mu dama can a jahohin  Yobe da Borno mun dade cikin wannan doka sama da shekaru biyu, domin duk yayin da ka samu kanka a cikin halin kunci ta yadda baka da sukunin aiwatar da wani abu naka, ba tare da samun umarni ba, to labudda a cikin dokar ta-baci kake, kamar yadda muke. Don haka mu dokar ta-baci ba sabon abu ba ne gare mu.
Alal hakika kusan za a iya cewa wannan doka da shugaban kasa ya sa, ai kusan an makaro, don bai ma dace dalilin da yasa aka sa wannan doka an bar shi ya zo ya zuwa  yanzu ba, kamata ya yi a ce tuntunin an magance matsalar, tun da gwamnati na da karfin soja da ’yan sanda, wanda za ta iya amfani da su wajen magance duk wata irin tashin-tashina da ta taso, ba sai ta kusan cinye rayukan al’umma da  dukiyoyinsu ba.
Mu dattawan mun sha yin tarurruka, tare da tattauna wannan lamari da ke addabarmu, yadda muke fuskantar gwamnatin tarayya da batun tun ma lamarin bai kai hakan ba, amma aka gaza daukar wani kwakkwaran matakin, shi yasa yanzu da al’amuran suka kai ga matakin tabarbarewa har  an kusan makarowa dangane da daukar matakin magance shi, ko da yake mai yiwuwa a lokacin ana zaton ko wannan rikita-rikita ta tsaya ne kawai a jihohin da gwamnatin tsakiya ba ta ganin kimarsu, wato Borno da Yobe; ko kuma Arewa kawai, shi ya sa mutanen kudu ke ganin bai shafe su ba. Don haka suke adawa da samun bakin zaren tun da wuri. Sun manta da cewar masifa irin wannan in ta taso ba ta tsayawa ga bangaren kasa kawai ba, sai ta kai ga game dukkan kasa in ba a yi hattara ba. Da yake lamarin yanzu ya kai ga babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, da saura jihohin makwabta da ma wani bangare na kudanci, to sai yaya?
Kuma ma mu abin da ke daure mana kai shi ne, yadda har ya zuwa yanzu gwamnatin tarayya ta gaza yi mana bayanin wuraren da wadannan ‘yan kungiya ke samun manya-manyan makamansu na yaki ko wurin da suke, duk da dimbin jami’an tsaron asiri da na sarari da kasar nan ke tunkaho da su.
A ganina gwamnati da gangan ta ke yi akan wai ba ta san su ba. Wannan mataki da gwamnatin ke dauka in an yi sa’a a dace ya yi amfani, in kuma ba a yi sa’a ba, a sake dagula lamarin. Don ba a magance rikita-rikita da amfani da wuta, ma’ana wuta da wuta ba ta magance duk wani hargitsi, sai da hawa kan teburun shawara. Saboda an yi amfani da irin wannan hikima  a kasashen duniya masu tarin yawa, amma kuma baa kai ga nasara ba, a karshe dole sai an hau teburin sasantawa.
Abin da muke jin tsoro shi ne, sari-ka-noke,  don za a iya  cewa an kawo karshen Boko Haram gaba daya, amma in aka bar biyu zuwa uku cikinsu, to sukan iya sake tada kayar baya, ta yadda za su sake dagula lamarin.
Don in za a bada tarihin Boko Haram daga shugabansu Muhammad Yusuf za a fara, wanda ’yan sanda suka kashe shi tunda an ce sojoji  a raye suka kama shi, da aka kawo shi, maimakon a hukunta shi, sai kawai aka harbe shi, tun daga lokacin magoya bayansa suka ce ba su yarda ba. Wannan ne sanadin samun kanmu cikin irin wannan ukuba. Amma abin da nake nufi jami’an tsaro su tashi don sanin musabbabin wannan rikici, saboda idan baka san tushen matsala ba, to da wuya ka iya samun nasara magance ta da wuri, sai ido yayi ja.
Aminiya: Kana nufin wannan doka ba ita ce mafita ba ke nan, to ina mafita a matsayin ku na dattawan wannan yankin?
Khalifa: To da farko dai zan  ce abin da za mu kira mafita shi ne, komawa ga Allah (SWT), tare da addu’ar Allah Ya kawo karshen wannan matsala. Na biyu kuwa kasancewar dokar ta-baci tsarin mulki ya tanadi watanni shida ne, in abu ya ki ci a a kara lokaci ko kuma a ce an dage ta dungurungum, balle wannan dokar da ba ta shafi ’yan siyasar da ke mulkin jihohin ba, kowannen su yana kan kujerar sa, illa dai harkokin tsaro ne aka karbe daga hannunsu, aka mika su ga masu shi, wato hukumomin tsaron soja da ’yan sanda, ka ga a she in ba su samu nasara ba, ai muna cikin tsaka mai wuya ke nan shi ya sa na ce addu’a ita ce babbar mafita, da kuma darewa kan teburin shawara, don ko yaki ne tsakanin kasa da kasa, ana hawa teburin shawara ballantana tsakanin ’yan kasa da gwamnatinsu, duk da cewar gwamnatin tarayya ta ce ta kafa kwamitin sasantawa da yin afuwa.
Aminiya: Me za ka ce game da kwamitin sasantawa tare da yin afuwa da shugaban kasa ya kafa kafin sa dokar ta-bacin?
Khalifa: Kai tsaye wannan kwamiti a ganina aikinsa ai ya kare, domin babu yadda za a yi a ce yau ka kafa kwamitin yin afuwa da sasantwa, a daya gefen kuma aka wayi gari ka kafa dokar ta-baci, don damke mutanen da ka ce ka kafa kwamiti. Kuma ya sasantwa za ta yiwu, alhali ka kama 10 ka ce ka kashe, ka kama 60 da ‘yan kai ka ce ka garkame, to me kake zato? Kana tsammani wadanda ka ce su zo a sasanta za su zo? Ban yi tsammani ba. Don kwamitin sasantawa da yin afuwa da kuma sa dokar ta-baci duk akan abu guda ne, taura biyu kuwa ai bata taunuwa.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50