Dokar ta baci: Izala ta bukaci jami’an tsaro su guji musguna wa jama’a
Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS), ta bukaci Jami’an tsaro, musamman wadanda ke gudanar da ayyukan samar da tsaro a jihohi uku da gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta-baci da su guji cin zarafi ko musguna wa jama’a a yayin gudanar da ayyukansu, ta kuma bukaci al’umman musulmi na kasa baki daya da […]
Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS), ta bukaci Jami’an tsaro, musamman wadanda ke gudanar da ayyukan samar da tsaro a jihohi uku da gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta-baci da su guji cin zarafi ko musguna wa jama’a a yayin gudanar da ayyukansu, ta kuma bukaci al’umman musulmi na kasa baki daya da su yi azumi na musamman tare da kara kaimi wajen gudanar addu’o’in na kunutu a masallatai domin gushewar matsalar tarzoma da wadansu sassan Najeriya suka samu kansu a ciki.
Shugaban kungiyar na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala taro na kwana biyu da kungiyar ta gudanar a birnin Abuja, a yayin da ya ke zantawa da Wakilinmu.
Sheikh Abdullahi Bala Lau, wanda ya jagoranci zaman da ya kunshi ’yan majalisar zartarwa ta kasa ta kungiyar, ya kuma bukaci al’ummomin da ke zaune a jihohin da dokar ta-bacin ta shafa da su kasance masu hakuri. Ya ce, “fitina idan ta taso ba a san inda za ta tsaya ba, kuma ina ganin irin hakan ne ya shafi Jihar Adamawa, batun danganta dokar ta-baci a jihar da siyasa ko akasin haka, duk ba zai samar mana da mafita ba. Ya kamata mazauna Jihar su dauki al’amari a matsayin kaddara kamar yadda ya shafi ’yan uwanmu da ke Jihohin Borno da Yobe. kuma abin da bangaren tsaro ya hango har ya kai aka sa Jihar a cikin rukunin dokar ta-baci, ba lallai ne jama’a da ke zaune a jihar su fahimci dalilin ba.