Dokar Ta-baci na barazana ga harkar noma a Yobe -Manoma
Duk da cewar damina ta fara kankama a sassan Jihar Yobe, akwai yiwuwar harkokin noma a daminar bana su samu nakasu a yankunan karkara da sakamakon dokar ta-baci da jihar ke fuskanta saboda akasarin manoman na tsoron fita daji don yin aikin gona don kauce wa jami’an tsaro da ke farautar ’ya’yan kungiyar Boko Haram.Aminiya […]

Duk da cewar damina ta fara kankama a sassan Jihar Yobe, akwai yiwuwar harkokin noma a daminar bana su samu nakasu a yankunan karkara da sakamakon dokar ta-baci da jihar ke fuskanta saboda akasarin manoman na tsoron fita daji don yin aikin gona don kauce wa jami’an tsaro da ke farautar ’ya’yan kungiyar Boko Haram.
Aminiya ta gano cewa shakkun da manoman jihar ke nunawa ya sa manoma da yawa na iya kaurace wa noma don tsoron abin da ke iya faruwa gare su, ganin cewa akasarin wadanda ake zargin ’ya’yan kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah Lid Dawa’ati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram sun kaurace wa manyan birane, inda suka tare a yankunan karkara kamar yadda jami’an tsaron ke nunawa, kuma hakan ya sa jami’an tsaro na JTF ke kai mafi yawan samamensu a yankunan karakara da suke cewa kwalliya na biyan kudin sabulu.
Manoma da dama da Aminiya ta zanta da su ne suka bayyana haka a Damaturu. Wani manomi mai suna Malam Adamu Guya ya ce sun fara samun ruwan sama kusan mako uku amma kuma tsoron fita daji don aikin gona saboda gudun haduwa da jami’an tsaro ya sa sun kasa fita. Ya ce a ganinsa da kyar su yi noma a bana saboda tsoron ransu.Ya ce, a kullum suna kwana da tashi da fargabar yadda za su yi su gudanar da aikin gona, duk da ba abin da suka sani sai noma a rayuwarsu.
Sai ya roki gwamnati ta kokarta samar musu da yanayin da za su bi don gudanar da aikin noma ba tare da fargaba ba musamman ta wajen jan hankalin jami’an tsaro su kauce wa kama wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.
Duk kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin kakakin rundunar JTF a Jihar Yobe Laftana Eli Lazarus don jin ko yaya za su yi da wannan koke na manoma ya ci tura kasancewar babu wata hanyar tuntuba sakamakon katse hanyoyin sadarwa a jihar.