Dokar Takaita Wa’azi ta Jihar Kaduna

Yan mintuna kadan kafin tsohon Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna, Aminu Abdullahi Shagali ya bayyana kawo karshen wa’adin majalisar ne, Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince tare da tabbatar da dokar takaita wa’azi a jihar. Shagali ya ce za a kuma kafa wata hukuma ta hadakar addinai wadda Gwamna zai nada mata shugaba da […]

Dokar Takaita Wa’azi ta Jihar Kaduna
Dokar Takaita Wa’azi ta Jihar Kaduna

Yan mintuna kadan kafin tsohon Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna, Aminu Abdullahi Shagali ya bayyana kawo karshen wa’adin majalisar ne, Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince tare da tabbatar da dokar takaita wa’azi a jihar. Shagali ya ce za a kuma kafa wata hukuma ta hadakar addinai wadda Gwamna zai nada mata shugaba da kuma wakilai biyu wadanda za su wakilci addinin Musulunci da addinin Kirista.

Haka kuma a karkashin wannan doka za a samar da kwamiti na hadakar addinai a dukkan kananan hukumomi 23 da ke jihar. Kudirin dokar yana kunshe da cewa duk wanda ya kunna kaset na wani abu da ya shafi addini da kara sosai ko kuma ya bude lasifika da kara a wajen da jama’a suke ban da masallaci da coci daga karfe 11 na dare zuwa karfe 4 na dare ya aikata laifi. Don haka zai iya fuskantar dauri na a kalla shekara 2 ko tarar Naira dubu 200 ko a hada masa duka biyun.

Dokar ta ci gaba da cewa duk wanda ya ci mutuncin wani a bainar jama’a ko ya yi wasu kalamai na batanci ko na karya ga wani addini wadanda za su iya haddasa tashin-tashina zai fuskanci dauri na akalla shekara 6 ko tarar Naira dubu 100, ko a hada masa duka biyun.

Wannan kudiri wanda aka gabatar tun a shekara 3 da suka gabata, kwaskwarima ce da aka yi wa wata doka da dama aka yi ta tun a 1984. Domin kare rayuka da kuma dukiyar jama’a daga salwanta sakamakon abin da batanci da kuma wa’azi barkatai ke haddasawa ne Gwamnan Soja na wancan lokaci Iya Kwamanda Usman Mu’azu ya yi dokar bisa kudirin dokar soja Mai lamba 7 a cikin watan Agustan 1984 don takaita wa’azi. Kamar yadda bayanin dokar ya ce; “Dalilin wannan doka shi ne ba da dama ga masu ilimin addinai kadai su gabatar da wa’azi a cikin fadin jihar.”

Jim kadan bayan gabatar da wannan kudirin dokar a gaban Majalisar Jihar a shekarar 2016, kudirin ya yi ta samun suka daga malaman addinai daga bangaren Musulmi da Kirista wadanda suke gani cewa dokar karan-tsaye ne ga ’yancin dan kasa na bin addini da kuma fadar albarkacin baki. Tsohon Mai bai wa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Patrick Yakowa Shawara kan Harkokin Addinin Musulunci, Sheikh Haliru Abdullahi Maraya tun da farko ya shawarci Gwamna El-Rufa’i da kada ya sanya hannu a wannan doka domin a cewarsa “Sashe na 38 (1) karamin sashe na 1 ya tabbatar wa ’yan kasa ’yancinsu na yada manufofin addinansu matukar dai bai ci karo da Kundin Tsarin Mulkin Kasa ba.”

Wadanda suke ikirarin cewa wannan doka an yi ta ce don takaita addinai, ba su fahimci dokar ba, saboda makasudin dokar shi ne ta tabbatar da ingancin masu wa’azi a bainar jama’a. Amma a ce wai an yi ta ce don dakile addinai zance ne na karya kuma marar tushe. Saboda dokar za ta ma tabbatar da girmama juna a tsakanin addinai daban-daban da ake da su a jihar. Ganin yadda addini ya kasance wata kafa da ake amfani da ita don tunzura wadansu marasa kishi wajen tayar da zaune-tsaye a wasu sassa da kuma fadin  Najeriya, hakika fadace-fadacen kabilanci da na addini da aka yi ta samu a cikin shekaru wajen 30 da suka wuce shi ne makasudin da ya sanya Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta sanya hannu a kan wannan doka. An salwantar da rayukan jama’a da dama tare barnatar da dukiyoyi na dubban miliyoyi a fadace-fadacen kabilanci da wadansu masu tsaurin ra’ayi wadanda ba su fahimci dokokin addinansu ba suke haddasawa.

Duk da haka, ya kamata a aiwatar da wannan doka tare da yin taka-tsantsan. Mambobin wannan kwamiti tun daga matakin jiha har zuwa na kananan hukumomi ya kamata su yi adalci wajen tantancewa da kuma ba da lasisin yin wa’azi ga wadanda suke neman yin wa’azin. Sannan su kau da son kai da son zuciya wajen gabatar da ayyukansu su tabbatar ba su dakile wadanda suka cancanci a bar su yi wa’azin ba.

Idan har Gwamna El-Rufa’i ya sanya wa wannan doka hannu, wannan wata dama ce ta kawo karshe fitinar da ta ki ci ta ki cinyewa a wannan bangare na kasar nan. Don haka muna kira da babbar murya ga Gwamnan da ya sanya wa wannan doka hannu ba tare da bata lokaci ba.