Dokar tsarin kudi ta Bankin CBN na samun nasara- Farfesa Uwaleke

Farfesa Uche Uwaleke shi ne Farfesan Najeriya na farko a fannin ilimin kasuwar hannun jari kuma shi ne Shugaban Sashen Banki da Kudi na Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi. A tattaunawar da ya yi da wakilinmu, Sunday Ogwu ya bayyana cewa daidaiton da aka samu a bangaren tattalin arziki daga tushe wata alama ce […]

Dokar tsarin kudi ta Bankin CBN na samun nasara- Farfesa Uwaleke

Farfesa Uwaleke

Farfesa Uche Uwaleke shi ne Farfesan Najeriya na farko a fannin ilimin kasuwar hannun jari kuma shi ne Shugaban Sashen Banki da Kudi na Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi. A tattaunawar da ya yi da wakilinmu, Sunday Ogwu ya bayyana cewa daidaiton da aka samu a bangaren tattalin arziki daga tushe wata alama ce da ke nuna karfin gwiwar da ake da shi kan tsarin kudi na Bankin CBN. Ga yadda hirar ta kasance:

Bari mu fara jin ra’ayinka kan sakamakon taron tsarin dokar kudi wanda shi ne na farko a bana. Me ya sa kake tunanin taron bai rage darajar kudi ba tun watan Yulin shekarar 2016?

Bari in fara da cewa matakin da kwamitin ya dauka na bai-daya a wannan lokaci bai bayar da mamaki ba saboda dalilai masu yawa da zan bayyana nan gaba. Hakika kamar yadda ka ambata adadin kudin ruwa wanda shi ne adadin da kwamitin ya amince da shi ya dore da kashi 14 cikin 100 tun watan Yulin shekarar 2016.

Ni a ra’ayina adadin da aka yanke zai bunkasa bayar da bashi ga bangarori, zai rage yawan kudin da kamfanoni da ma’aikatu suke kashewa wanda hakan zai kai ga samar da ayyukan yi masu yawa, zai bunkasa kasuwar hannun jari da kuma tallafawa wajen rage rashin biyan bashi a bankuna. Saboda haka zai taimaka wa kudi da kuma karfin gwiwar kasuwanci. Tambayarka ta dalilin da ya sa kwamitin kudi bai yanke adadin kudin ruwa ba a watannin baya tana kan turba musamman ma idan aka yi la’akari da raunin da ake da shi na ci gaban tattalin arziki, amma bari mu yi bayani dalla-dalla.

Da farko, yana da muhimmanci mu fahimci cewa idan aka zo tsara dokokin kudi, Bankin CBN kamar kowane babban banki zai rika fama da abin da ake kira ‘Policy Trilemma’ wanda yake nuna iyakacin ikon da ke gare shi. Idan muka yi la’akari da ainihin ikon da bankin yake da shi na daidata farashi, zai zama wani abu mai wuya ga bankin ya rage tashin farashi da karin kudin ruwa da daidaita farashin kudi da karin kudin ajiya na kasashen waje a lokaci guda. Saboda haka yanke farashi zai shafi ci gaban da aka samu a fannin daidaton farashin darajar kudi wanda shi ne matakin cimma rage tashin farashi. Yana da matukar kyau mu fahimci cewa tashin farashin yana aukuwa ne sakamakon tashin farashin fitar da kayayyaki saboda tashin darajar kudi. Ragin yana nufin faduwa a tsari wanda zai sanya matsi ga darajar kudi da kuma janyo tashin farashi. Tashin farashi a yanzu na kashi 11 da digo 44 cikin 100 ya saba wa matsayar Babban Banki ta kashi tara cikin 100.

Dadin-dadawa, ragin tsarin kudi zai janyo fitar da jari zuwa wajen kasar don neman riba wanda hakan zai shafi kudin ajiyarmu na kasashen waje. Saboda kudin ajiyarmu na kasashen wajen ya dogara ne da jarin da za a shigo da shi kasar  na hada-hadar kasuwancin da ake yawan bukata. Alakar wannan ga tattalin arzikinmu mai rauni shi ne akwai masana da suke goyon bayan cewa shi farashin kudin ruwa batu ne da ke yin kasa. Abin nufi shi ne ragin adadin farashi a kashin kansa ba ya nuna karin bashi musamman ma ga tattalin arziki. A baya ragin kudin ruwa ya kasa rage bayar da bashi ga bangaren da ba na gwamnati ba saboda bankuna suna da abubuwan da suke fama da su.

Idan ka dubi hada-hadar kudin wasu bankuna a Najeriya akwai alamun bankuna na fuskantar barazana musamman a yanzu da suke fama da yawan rashin biyan bashi da karin kudin tafiyar da ayyuka da kamata ya yi a rage farashi wanda zai daidaita wannan kari maimakon yin ragi ga masu karbar bashi. Wannan shi ne ainihin kalubalen.

Tunda kasar nan ta fita daga masassarar tattalin arziki an cimma daidato a bangaren tattalin arziki wanda hakan yana da alaka da tsarin dokar kudi. Baya ga haka farfadowar farashin danyen mai da bullo da tallafin masu zuba jari da masu fitar da kaya da sanya iyakar samun kudin musaya na kasashen waje wanda Bankin CBN ya sanya kan abubuwa 42 ya taimaka kwarai wajen bunkasa asusun ajiyarmu na kasashen waje. Wannan ci gaba ya kawo daidaiton farashi a dukan bangarori kasuwar musayar kudi kuma ya taimaka wajen bunkasa masana’antu kamar yadda kididdiga ta nuna. Me ya rage kuma a yanzu shi ne tashin farashin kaya ya daidata daga kashi 18 da digo 72 cikin 100 a watan Janairun shekarar 2017 zuwa kashi 11 da digo 44 cikin 100 a watan Disamban bara. Saboda haka za a iya cewa daidaiton da aka samu a fannin tattalin arziki wani kwarin gwiwa ne ga tsarin dokar kudi na Bankin CBN.

Yanzu ka ce tsarin ragin kudin ruwa ba zai yi tasiri ba ga ragin bayar da bashi a bankuna, shin hakan na nuna yadda kudi masu yawa suke zagaywa a wajen bankuna?

Babu shakka, na fadi  wasu abubuwa da suka kama daga rashin tsaro, rashin kayan more rayuwa kamar karancin wutar lantarki da hanyoyin sufuri. Hakan yana da alaka da yadda ake da kudi a wajen banki wanda hakan ke nuna kalubalen da ake fuskanta a hada-hadar kudi ta bai-daya. Za ka yarda da ni cewa amfanin hada-hadar kudi na bai-daya ba ya misaltuwa. Akwai binciken da ya nuna cewa kasashen da ke da yawan hada-hadar kudi ta bai-daya suna da daidaiton tattalin arziki. Bankin CBN ne ke kokarin magance wannan kalubale. Idan za a iya tunawa kwanaki kadan da suka gabata, Bankin CBN ya kaddamar dabarar hada-hadar kudi ta bai-daya ta kasa baki daya. Babban manufar wannan tsari shi ne rage yawan balagaggu ’yan Najeriya wadanda ba sa cikin tsarin hada-hadar kudi ta bai-daya da kashi 20 cikin 100 nan da shekarar 2020 daga kashi 46 cikin 100 a shekarar 2010.

Don cimma wannan manufa, ya zama wajibi a magance manyan kalubalen hada-hadar kudi. Hakan ya hada da kalubalen bangaren tattalin arziki wanda ya hada da rashin kayan more rayuwa wanda yake janyo tsadar hada-hada da rashin riba ga masu samar da hada-hadar kudi ta bai-daya, rashin tsaro a wasu yankunan kasar nan musamma yankin Arewa maso Gabas wanda ya shafi rayuwar manoma a yankin wadanda suke su ne mafi yawan mutanen yanki da karancin dillalan da za su samar da yanayin da zai ba su damar tsarin hada-hadar kudi a yankunan karkara.

Har yanzu a kan tsarin dokokin kudi, mutane da yawa har da Bankin Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) sun soki farashin musayar kudi da ake amfani da shi a maimakon Bankin CBN ya bari kasuwa ta yi halinta na yanke farashi daya na darajar Naira. Mene ne ra’ayinka dangane da haka?

Na bibiyi tattaunawar da masana suka yi kan masu goyon baya da wadanda ke sukar rashin daidaiton darajar Naira wanda ba kamar yadda a yanzu ake tattala rashin daidaiton ba inda aka bar darajar Naira ga yadda kasuwa ta yanke. Masu goyon bayan farashin ya rika yin tangal-tangal sun musanta cewa idan aka bari farashin yana juyawa ainihin farashin Naira zai fito fili wanda hakan zai kai ga hade farashin gwamnati da kasuwar bayan fage. To amma abin takaici Naira tana da wani yanayi na daban. Idan ma barin farashin ya rika juyawa zai magance farashi daban-daban to ba zai magance kalubalen faduwa ba. Saboda kasar na shigo da mai da kayayyakin da ake sana’antawa da abinci kai muna shigo da komai, farashin kayan abinci zai yi tashin gwauron zabo saboda farashin musayar kudi kuma zai tilasta wa Bankin CBN ya tsaurara dokar kudi.

A matsayinka na Farfesan kasuwar hannun jari, ina kake jin kasuwar hannun jari ke fuskanta a shekarar 2019. Shin tsarin dokar kudi na da rawar da zai taka wajen daga darajar kasuwar?

A matsayinka na dan jarida kan fannin harkokin kudi, na tabbata ka san sakamakon kasuwar hannun jarin Najeriya a bara ba ta yi abin da ya kamata ba tunda har yanzu kididdiga na nuna rashin gamsuwa. Kasuwar ta yi asarar kashi 18 cikin 100 wanda yana da muhimmanci idan ka kwatanta da ribar da aka ci ta fiye da kashi 42 cikin 100 a shekarar da ta gabace ta. Abubawa biyu manya ne suka janyo wannan rashin tabuka komai. Na farko daga waje yake, wato saboda karin kudin ruwa da Gwamnatin Amurka ta yi wanda ya janyo karin tagomashi ga Amurka. Na biyu daga cikin gida ne wanda ya faru daga rashin tabbas na siyasa a Najeriya. Wadannan abubuwa biyu su ne suka janyo ficewar masu zuba jari na kasashen waje suka bar masu zuba jari na gida.