Doke Bayern Munich ya karfafa mana gwiwa – Arsene Wenger
Kocin kulob din Arsenal da ke Ingila Arsene Wenger ya ce doke kulob din Bayern Munich da ke Jamus da ci 2-0 a gasar cin kofin zakarun Turai (Champions League) a ranar Talatar da ta gabata ya karfafa musu gwiwar za su taka muhimmiyar rawa a gasar. Arsenal dai ta doke Munich ne da ci […]
Kocin kulob din Arsenal da ke Ingila Arsene Wenger ya ce doke kulob din Bayern Munich da ke Jamus da ci 2-0 a gasar cin kofin zakarun Turai (Champions League) a ranar Talatar da ta gabata ya karfafa musu gwiwar za su taka muhimmiyar rawa a gasar.
Arsenal dai ta doke Munich ne da ci 2-0 ta wajen ’yan kwallonta Oliber Giroud da Mesut Ozil a wasan da miliyoyin ’yan kallo suka kalla a sassan duniya.
Kafin wasan fiye da kashi 70 na masu sha’awar kallon kwallo sun yi hasashen Bayren Munich ne zai samu nasara a wasan musamman ganin yadda kulob din yake tashe inda ya lashe wasannin 12 a jere kafin wasan amma sai ya sha mamaki bayan Arsenal ta lallasa shi da ci 2-0. Kafin wasan Arsenal ta samu rashin nasara a wasanni biyu da ta yi a gasar al’amarin da ya sa ta dage don ganin ta samu nasara a wannan karo.
“Na ji dadin ganin yadda ’yan kwallonmu suka farfado da martabarmu a wannan gasa kuma ina da yakinin za mu yi rawar gani a bana”, inji Wenger.
Yanzu kungiyoyin biyu za su sake haduwa ne a ranar Laraba 4 ga watan Nuwamban wannan shekara a wasa zagaye na hudu watau nan da makwanni biyu masu zuwa.
Har yanzu Bayern Munich ce kan gaba a rukunin F da maki 6 daga wasanni uku, yayin da Olympiakos ke biye da maki 6 sai Dinamo Zagreb mai maki 3 sai Arsenal mai maki 3.