Doki ya kwanta a kan gawar wanda ya mallake shi yana kuka

Wani doki mallakar marigayi Wagner de Lima Figueiredo da ya rasu kuma ake shirin binne shi, ya sanya ’yan uwan mai shi  cikin tausayi bayan da ya  je kusa da gawar ya dora kansa a kan gawar yanazubar da hawaye don nuna alhinin wannan babban rashi. Dokin mai suna Sereno ya bai wa ’yan uwan […]

Doki ya kwanta a kan gawar wanda ya mallake shi yana kuka

Doki Sereno a jikin akwatin gawar maigidansa

Wani doki mallakar marigayi Wagner de Lima Figueiredo da ya rasu kuma ake shirin binne shi, ya sanya ’yan uwan mai shi  cikin tausayi bayan da ya  je kusa da gawar ya dora kansa a kan gawar yanazubar da hawaye don nuna alhinin wannan babban rashi.

Dokin mai suna Sereno ya bai wa ’yan uwan Wagner mamaki, inda hakan ya sa dan uwan Wagner, mai suna Wando de Lima  ya tafi da dokin makabartar da za a binne Wagner a garin Paraiba da ke Arewa maso Gabashin kasar Brazil.

Rahoto ya ce, dokin da Wagner sun yi matukar shakuwa, kamar yadda wadanda suka san su tare suka bayyana.

Mista De Lima ya ce, dubban jama’a sun ta wallafa wannan shakuwar da dokin ya yi da Wagner a shafukan Intanet. Ya ce, “Kamar dokin ya san Wagner ya rasu don haka yake ta yi masa ban-kwana, saboda wannan dokin na yi wa Wagner duk abin da yake so.”

Wagner de Lima Figueiredo ya rasu ne a hadarin babur lokacin bukukuwan sabuwar shekara bayan da babur din ya kwace masa yana kansa a birnin.

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo

China za ta sayar wa Elon Musk TikTok saboda rashin tabbas