Dokokin fim sun raba kan hukuma da ’yan fim din Hausa
Dokokin fim sun raba kan hukuma da ’yan fim din HausaFitar da wasu dokoki da Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta yi, bai yi wa yawancin masu shirya fina-finai dadi ba, kasancewar mafi yawan dokokin sun ci karo da yadda aka saba gudanar da fim yau da kullum.A wani taron tattaunawa da masu ruwa-da-tsaki […]
Dokokin fim sun raba kan hukuma da ’yan fim din HausaFitar da wasu dokoki da Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta yi, bai yi wa yawancin masu shirya fina-finai dadi ba, kasancewar mafi yawan dokokin sun ci karo da yadda aka saba gudanar da fim yau da kullum.
A wani taron tattaunawa da masu ruwa-da-tsaki a harkar fim, hukumar ta fto da wasu dokoki da ta ce akwai bukatar duk wani fim da za a yi sai an gabatar mata da labarin don tacewa kafin ma a kai ga daukar fim din. Haka kuma akwai bukatar mai fim ya mika shi ga kwararru don samun shawarwari kan yadda zai yi fim din don su dace da yadda ake yin fim a fadin duniya.
Mafi yawan masu fim din na ganin cewa dokokin na hukumar ba za su haifar wa masana’antar tasu da mai ido ba, domin dokoki ne da za su kai ta ga tabarbarewa.
A cewarsu, akwai bukatar hukumar ta sake zama ta duba dokokin tare da yi musu gyara ta yadda za su ba masu sana’ar fim din damar yi wa hukumar biyayya sau-da-kafa.
Wata dokar na bayani ne game da yadda ya kamata mata su sanya tufafi yayin fitowa a fina-finai, inda hukumar ta ce ba za ta sake lamintar shigar tsiraici a fina-finai daga matan ba, koda kuwa fitar da gashin kan mace waje ne. Har ila yau wata dokar na cewa dole ne mai fim ya nemi izinin fita daukar fim kafin ya fara daukar fim dinsa a ko’ina da sauran dokoki wadanda ’yan fim din ke ganinsu a matsayin tarnaki ga gudanar sana’arsu.
Wani fitaccen furodusa da ya nemi a boye sunansa, ya bayyana wa Aminiya cewa wannan abu da hukumar ta dauko, hanya ce marar bullewa domin a cewarsa: “Yaushe hukumar za ta iya gudanar da wannan aiki? Wane lokacin karanta labari take da shi? Idan aka ce haka za a bi, to za a dade ba a fitar da fim daya ba.”
Ya kara da cewa, “Game da batun fitowar mata a fim, to yaya za a yi a nuna matar da take karuwa ce ko gantalalliya a fim? Ko kuma yaya za ka yi da matar da ta zo a fim din a matsayin mai wani addinin da ba na Musulunci ba ko kuma wata kabilar? Ya kamata hukuma ta fahimci wannan kafin ta kai ga yanke hukunci. Idan kuma ba haka ba, sai mu koma gidan jiya wato mu yi kaura mu rika fita wasu jihohin muna yin fim. Wanda duk ya kawo fim dinsa Kano shi ya jiyo wa kansa,” inji furodusan.
Shi ma wani darakta da ya nemi a boye sunansa, ya ce fita daukar fim ba kullum ake yi ba, wani fim din za a dade ana daukarsa kafin a kai ga hada shi. “Kowa ya san ba a rana daya ake kammala daukar fim ba, to ana nufin duk ran da mutum zai fita daukar fim sai ya sanar da hukumar ko kuwa yaya abin yake? Ya kamata hukumar ta fito ta yi mana bayani. Idan aka ce kullum mutum zai fita daukar fim sai ya nemi izini, gaskiya an zo da son zuciya, domin abu ne da ba zai yiwu ba,” inji Daraktan.
Aminiya ta tattauna da Baba karami, wanda shi ne shugaban kungiyar Masu Shirya Fina-Finai ta Arewa ta kasa (AFMAN), ya ce ’yan fim mutane ne masu biyayya wadanda a kowane lokaci suke shirye su bi abin da hukuma ta zo da shi. A cewarsa za su yi dubi a tsanaki ga dokokin hukumar, idan suka ga wasu dokokin sun yi tsauri gare su, za su nemi hukumar ta sassauta musu. “Mu mutane ne masu bin doka da oda. Duk dokkokin da muka ga sun yi mana tsauri wajen yin amfani da su, to cikin kwantar da kai za mu nemi hukuma ta sassauta mana su,” inji shi.
A martaninsa Shugaban Hukumar Tace Fina-Finan, Malam Isma’ila Na’abba Afakallah ya ce wadannan dokoki da ake magana a kansu, ba wasu sababbi ba ne, suna nan tun shekarar 2001. “Idan mutane za su yi mana adalci, za su ga cewa duk dokokin nan babu wata sabuwa da muka fitar bayan zuwanmu, dokoki ne tun na shekarar 2001. Sai dai cewa a wancan lokaci dai an yi sako-sako da su ne kawai,” inji shi.
Ya ce idan har masu fim za su kai wa hukumar labarin fim dinsu ta tace, to zai sauwake musu irin asarar da za su iya yi bayan sun yi fim din. “Wannan abin da muke yi muna yi ne don jin dadin masu fim din, domin duk wanda ya kawo labarin fim dinsa aka tace masa tun kafin ya fita ya fara daukar fim, hakan zai rage masa kashe kudin da suke yi a wajen daukar fim. Hakan kuma zai rage asara ga mai fim, wanda sai bayan ya dauki fim dinsa sannan hukumarmu ta sa shi ya cire wasu wuraren a ciki ba,” inji Afakallah.