Dokokin gyaran haraji sun tsallake karatu na biyu a majalisa
Mataki na gaba shi ne miƙa ƙudirin ga kwamitocin majalisar domin ƙara yin nazari.
Dokokin Gyaran Haraji sun tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilai, bayan tafka muhawara mai zafi a tsakanin ’yan majalisar.
Tun da farko, an gabatar da ƙudirorin guda huɗu wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar, amma an haɗe su zuwa guda ɗaya domin sauƙaƙa nazari a kansu.
- An yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga a Kaduna
- Ɗan majalisar Kebbi ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC
Jagoran majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere ne, ya jagoranci tattaunawar, inda ya jaddada buƙatar sauta tsarin harajin Najeriya.
Ya ce dokokin za su sauƙaƙa biyan haraji, cire harajin kayayyakin buƙatu na yau da kullum kamar abinci da kiwon lafiya, tare da samar da rangwame ga ma’aikata masu ƙaramin ƙarfi.
Yawancin ’yan majalisar sun goyi bayan ƙudirin, inda suka ce hakan zai ƙara wa gwamnati kuɗin shiga tare da bunƙasa tattalin arziƙi ƙasa.
Sai dai wasu, kamar ɗan majalisa Sada Soli, sun nuna damuwa kan wasu sassa da ba a fayyace su ba a ƙudurorin, waɗanda ka iya haifar da matsaloli a nan gaba.
Duk da haka, bayan tattaunawa mai zurfi, majalisar ta amince da ƙudirin a karatu na biyu ta hanyar kaɗa ƙuri’a.
Mataki na gaba shi ne miƙa ƙudirin ga kwamitocin majalisar domin ƙara yin nazari, tare da gyara matsalolin da ke tattare da ƙudirorin.
Idan aka amince da shi, za a gabatar da shi a karatu na ƙarshe kafin ya zama doka.