Dokokin haraji barazana ne ga ma’aikata — NLC
Ajaero ya ce dole ne a janye dokokin saboda suna barazana ga zaman lafiyar ma’aikata.
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), ta buƙaci Gwamnatin Tarayya, ta janye dokokin haraji da ke gaban Majalisar Tarayya.
Shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero ne, ya bayyana hakan a sakonsa na sabuwar shekara ga ma’aikata.
- Mun kashe ’yan ta’adda 10,937 a 2024 – Sojoji
- Garin da mutum 10,000 ke ganin likita a ƙarƙashin bishiya a Kano
Ya jaddada buƙatar tattaunawa tsakanin dukkanin masu ruwa da tsaki don samar da dokar haraji da za ta bunƙasa ci gaban ƙasa kuma ta samu karɓuwa a wajen jama’a.
“Matsayarmu a bayyane take, dole gwamnati ta bai wa zaman lafiya a masana’antu muhimmanci ta hanyar mutunta yarjejeniyoyi da ƙungiyoyin ƙwadago tare da yin tattaunawa mai ma’ana,” in ji Ajaero.
“Dole ne a daina amfani da tashin hankalin ma’aikata da ƙungiyoyinsu saboda hakan na haifar da rikici.”
Hakazalika, Ajaero ya bayyana cewa ƙungiyar za ta sake duba albashi domin tallafa wa ma’aikata da ke fama da matsin tattalin arziƙi da manufofin gwamnati suka haifar.
“Mun dage cewa gwamnatoci a kowane mataki su tabbatar da bin dokar mafi ƙarancin albashi ta 2024 da kuma kyautata walwalar ma’aikata,” ya ƙara.
A cikin saƙonsa, Ajaero ya yi kira ga ’yan Najeriya da su haɗa kai wajen magance ƙalubalen ƙasa.
“Ƙalubalen rayuwa da muke fuskanta ba za su karya mana gwiwa ba.
“Sai da haɗin kanmu da ƙoƙarinmu ya ci gaba da jagorantar Najeriya zuws gaba,” in ji shi.
NLC na shirin gudanar da taron ƙasa a Ibadan, domin tattauna batutuwa da yin haɗin gwiwa wajen samo mafita don ci gaban ƙasa.