Dokokin Haraji: Matakin gwamnoni bai wadatar ba – Ndume
Ndume ya ce har yanzu akwai gaɓoɓin da ba a fayyace abin da suka ƙunsa ba.
Sanata Mohammed Ali Ndume, mai wakiltar Kudancin Borno, ya ce shawarwarin da Gwamnonin Najeriya (NGF), suka bayar kan sabbin dokokin haraji abu ne mai kyau, amma bai wadatar ba.
Ya bayyana cewa har yanzu akwai sassa na dokokin da ke buƙatar ƙarin bayani.
- HOTUNA: Tankar mai ta yi bindiga a Dikko Junction
- Gaza: Yadda za a yi musayar fursunonin Palasdinawa da Isra’ila
Dokokin, waɗanda ke gaban Majalisar Dokoki ta Ƙasa a yanzu, sun fuskanci suka, musamman a Arewacin Najeriya.
Mutane da dama na ganin dokokin ba su da adalci ga yankin Arewa, suna kuma kallonsu a matsayin wata maƙarƙashiya ta gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Sanata Ndume, wanda ya saba sukar manufofin gwamnatin, ya ce sauyin harajin zai ƙara jefa talakawa cikin wahala maimakon ya rage musu tsanani.
Ya yi kira ga shugaban ƙasa da ya janye dokokin.
A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Ndume ya ce, “Abin da gwamnonin suka yi abu ne mai kyau, amma bai wadatar ba saboda har yanzu ba mu fahimci dokokin gaba ɗaya ba.”
Ya buƙaci a ci gaba da yin tuntuɓa da tattaunawa tare da shigar da ra’ayoyin al’umma domin tabbatar da an yi gyare-gyaren da suka dace.
“Akwai buƙatar bayyana gaskiya a kan dokokin. Idan aka yi gaggawar aiwatarwa, za a yi kuskure,” in ji Ndume.
Ya ƙara da cewa yanzu an samu damar gyara kurakuran da ke cikin dokokin, ba kamar da ba, inda aka bar su ba tare da gyara ba.
Ya jaddada cewa ’yan majalisa da al’umma ne ke da alhakin gyara kurakuran da ke cikin sabbin dokokin a yanzu.