An sako Dokta Abdulaziz Idris Dutsen Tanshi daga kurkuku

Malamin ya isa gida, inda aka gan shi a majalisinsa mabiyansa sun shirya masa gagarumar tarba.

An sako Dokta Abdulaziz Idris Dutsen Tanshi daga kurkuku

Kotu ta sako Dokta Idris Abdul-aziz Dutsen Tanshi, bayan ta tsare shi a gidan gyaran hali.

Fitaccen malamin ya isa gida, inda aka gan shi a majalisinsa, mabiyansa sun shirya masa gagarumar tarba har ya gabatar da jawabi.

Kotun Majistare ta Jihar Bauchi, ta ba da belin Dokta Idris Abdul-aziz ne bayan da kama shi, bisa zargin sa da kalaman batanci ga Manzon Allah (SAW), zargin da ya musanta.

A kan rashin cika sharuddan ne kotu ta ba da umurnin a tisa keyar malamin zuwa gidan gyaran hali

Kungiyar Fityanul Islam ce dai ta maka malamin a Kotun Majistare da Jihar Bauchi, bisa zargin sa da kalaman batannci ga  Manzon Allah (SAW), zargin da malamin ya musanta.

Kotun ta bayar da belin fitaccen malamin ne bayan bukatar hakan da lauyoyin malamin suka nema.

A ranar Litinin ne, ’yan sanda suka gurfanar da Sheikh Idris Dutsen Tanshi bisa zargin tayar da hankulan jama’a.

A kwanakin baya ne wadansu kungiyoyin addini guda 17 karkashin kungiyar Fityanul Islam ta Najeriya, ta rubuta takardar koke ga kwamishinan ’yan sandan jihar, bisa zargin Malamin ya yi batanci ga Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammadu (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi).

Lamarin da ya sanya ke nan ’yan sanda suka gayyaci dukkan bangarorin da abin ya shafa kuma tun a makon jiya aka nemi malamin ya amsa goron gayyatar.

’Yan sanda sun gurfanar da malamin ne a Babban Kotun Majistare mai lamba ta 1 kan zargin da ake masa.

alkalin kotun ya hana bayar da beli, sannan ya bayar da umarnin a ajiye wanda ake kara a gidan gyaran hali, tare da bayar da umarin sake dawo da shi gaban kotu ranar Talata.

A watan da ya gabata ma malamin a cikin hudubarsa ta Azumin Ramadana, an zarge shi munana ladabi ga Manzon Allah (SAW).

Sai dai kuma an wasu malaman da suka goyi bayansa da cewa kalamansa na an turba ta gaskiya.

Lauyoyinsa sun shaida wa kotu cewa zargin da ake masa da aikatawa ba zai hana a bayar da shi beli ba, inda a ranar kotun kotu ta sanya Talata domin yanke a kan bukatar lauyoyin.

Sai dai a ranar alkalin kotun ya ba da umarnin a ci gaba da tsare malamin a gidan yari kafin zaman na ranar Talata.

Kotun ta bayar da belin malamin ne bisa sharuddain gabatar da wani babban ma’aikacin gwamnati da ya kai matakin babban sakatare da kuma mai unguwa ko hakimi su tsaya masa.

Za kuma su gabatar da takardar mallakar wata kadara da kimarta ta kai Naira miliyan biyar sannan dole ne masu tsaya masa su gabatar da hotunansu ga rijistaran kotu.

’Yan bindiga sun sace Farfesa, sun nemi N10m kuɗin fansa

Za a ɗauke wutar lantarki na tsawon mako 2 a Abuja

Hukumar tace fina-finai ta dakatar da Samha kan shigar banza

Sakataren Gwamnatin Ondo ya rasu bayan yin hatsarin mota