Dokta Aliyu Funtuwa ya zama wakilin Malaman Katsina
A ranar Asabar 31 ga Watan Maris na wannan shekarar ce ta zamo muhimmiyar rana mai dimbin tarihi da kuma farin ciki ga ‘yan uwa, abokan arziki da masoyan Dokta Aliyu Maikaji bisa la’akari da karamcin da fadar Mai Martaba Sarkin Katsina ta yi masa na nadin sarautarsa a matsayin Wakilin Malaman Katsina. Hakika wannan […]
A ranar Asabar 31 ga Watan Maris na wannan shekarar ce ta zamo muhimmiyar rana mai dimbin tarihi da kuma farin ciki ga ‘yan uwa, abokan arziki da masoyan Dokta Aliyu Maikaji bisa la’akari da karamcin da fadar Mai Martaba Sarkin Katsina ta yi masa na nadin sarautarsa a matsayin Wakilin Malaman Katsina. Hakika wannan nadi ya zo a daidai lokaci tare da yin sa bisa cancanta ga duk wanda ya san wanna karimin shugaba.
Don haka za mu iya cewa an ajiye kwarya a gurbinta, kuma ba abin mamaki ba ne domin ya cancanta bisa la’akari da irin gudunmawar da ya ke bai wa fannin ilmi a mataki daban-dabam. Hakika za a iya cewa Malaman Katsina su kwantar da hankalinsu don kuwa sun samu wakili na gari mai amana da ganin darajar mutane da girmama dan adam. Ana yi masa kyakkyawan zato da fatan zai gudanar da wakilci bisa jajircewar da aka sanshi ba tare da nuna bambanci ba.
Dokta Aliyu Idris Funtua, shi ne shugaban Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Jihar Katsina, mutum ne da ya yi shuhura wajen karamci, kima da girmama dan adam. Ya na bada gagarumar gudunmawa wajen ciyar da ilmi a matakai da dama kama daga ilmin zamani da na addini iya bakin kokarinsa.
Ya samu kyakkyawar shaida daga wurin al’umma musamman abokan aikinsa, dalibai da makwabtansa na rashin nuna kyama ko hantara ga duk wani mahalukin da yayi mu`amala da shi. Mutum ne mai addini da son sada zumunci a tsakanin dangi, abokai da sauran al`umar musulmi.
Tarihinsa
An haifi Aliyu Idris Funtua a garin Dandume da ke cikin Jihar Katsina. Ya yi karatun firamare a makarantar Aya da ke Funtua, da na sakandare a makarantar sakadaren gwamnati da ke garin Malumfashi. Ya wuce Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Katsina ya kammala a shekarar 1984. Ya yi digirinsa na daya da na biyu da kuma na uku a Jami’ar Bayero da ke Kano.
A shekarar 1985 Aliyu Idris Funtua ya fara aikin koyarwa. Ya yi aiki da ma’aikatar ilimi ta tsohuwar Jihar Kaduna da kuma ta Jihar Katsina. A shekarar 1997 ya samu aiki da Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Katsina. Ya rike mukamai da dama a wannan Kwaleji da suka hada da shugaban sashen nazarin Hausa, da daraktan sashen kasuwanci da tuntuba na Kwalejin, da mataimakin shugaban Kwalejin, da mukaddashin shugaban Kwalejin. A halin yanzu shi ne shugaban Kwalejin.
Aliyu Idris Funtua mamba ne na kungiyar marubuta ta kasa reshen Jihar Katsina da kungiyar harsunan Nijjeriya ta kasa da kungiyar masana ta kasa, da kungiyar malamai ta kasa, da kungiyar habaka ilimi ta kasa da cibiyar kwararrun ma’aikata ta kasa. Haka kuma babban edita ne na mujallar farfado da al’adun gargajiya Cultural Rebibal Magazine da kuma Kusugu Journal. Haka kuma a shekarar 2014, Dokta Aliyu Idris Funtua ya halarci kwas a kan fannin koyarwa na zamani a birnin Manchesta ta kasar Ingila.
Ya samu lambobin girmamawa daga kungiyoyi da dama da suka hada da ta Garkuwan Matasan Arewa wadda kungiyar matasan Arewa ta ba shi a shekarar 2016, da wadda kungiyar kabilar TIb ta Joseph Tarka ta ba shi ta mukamin Gbenda U TIb wato Sarkin yakin TIb saboda yaba masa bisa kula da kabilu a Kwalejinsa.
Ya kuma amshi irin wannan karramawa daga kungiyoyin ‘yan jaridu da na marubuta da na dalibai. A shekarar 2017 ce kungiyar dalibai Musulmi ta kasa ta ba shi mukamin Khadimul Fukara’a wato Jagoran marasa karfi da mabukata.
Aliyu Idris Funtua ya bayar da gagarumar gudummuwa wajen raya adabi da al’adun Hausawa da Fulani. A sakamakon kwazonsa da jajircewarsa ya samar da katafaren dakin adana kayan tarihi na al’adun Hausawa da Fulani, da dakin karatu, da kyauye na musamman da ya kunshi gidajen Hausawa da rugagen Fulani na al’ada a Kwalejin Ilimi ta Tarrayya da ke Katsina. Wadannan sun zama wuraren ziyara da tuntuba ga mutane ba a Nijeriya kadai ba, har da kasashe mabwabta musamman masana da masu nazari a kan adabi da al’adun Hausawa da Fulani.