Dokta Asabe: Maza su ne kalubalenmu

Dokta Asabe bilita Bashir, ita ce ’yar majalisa mai wakiltar mazabar Goza da Damboa Chibok a Jihar Barno. Aminiya ta samu tattaunawa da ita tare da jin yadda aka yi har ta tsunduma cikin harkokin siyasa da kuma irin kalubalen da ta fuskanta. Ga yadda hirar ta kasance: Za mu so ji takaitaccen tarihin ki?Da […]

Dokta Asabe: Maza su ne kalubalenmu
Dokta Asabe: Maza su ne kalubalenmu

Dokta Asabe bilita Bashir, ita ce ’yar majalisa mai wakiltar mazabar Goza da Damboa Chibok a Jihar Barno. Aminiya ta samu tattaunawa da ita tare da jin yadda aka yi har ta tsunduma cikin harkokin siyasa da kuma irin kalubalen da ta fuskanta. Ga yadda hirar ta kasance:

Za mu so ji takaitaccen tarihin ki?
Da farko sunana Dokta Asabe bilita Bashir, ina wakiltar mazabar Goza da Damboa Chibok a Jihar Barno. An kuma an haife ni a shekarar 1965, na yi makarantar firamare a kauyen Limankara da ke karamar hukumar Gwoza. Daga nan na wuce babbar makaranta a kwalejin Gwamnati da ke garin Maiduguri. Har ila yau, na yi jami’ar Maiduguri, na yi aikin yiwa kasa hidima na shekara daya. Daga nan na koma aiki  Jami’ar Maiduguri, na kara dora wani digiri har na kai matsayin digiri na uku , duk a jami’ar. A takaice dai na tashi a malamar makaranta amma, kamar yadda kowa ya sani, kai kana na ka Allah na na shi, har na zo na tsince kaina a siyasa.
Farkon tsayawa ta takarawa na fito takarar neman kujerar majalisar Goza, amma ban samu ba saboda rasuwan shugaban kasa margayi Sani Abacha, sai da aka kara kirkiro wasu jam’iyyu na sake yin takara dai-dai da wanda na yi a baya. Na yi nasara. Hakazalika, na taba yin kwamishina a ma’aikatu kamar na: kiwon lafiya,tsare-tsare da gine-gine, ma’aikatar saman da wutan lantarki da ma’aikatar harkokin mata, ma aikatar aikin gona da kuma ma’aikatar kasuwanci da masana antu. Har ila yau, a bana na yi takara kuma Alhamdulillahi, na yi nasara, ina wakiltan bangaren Goza da Damboa Chibok a Jihar Barno.
Me ye yaba ki sha’awar shiga siyasa?
Siyasa ba wani abin da za a ce ya baka sha’awa ba ne, ni yadda nake ji, shi ne kawai yadda Allah Ya kaddara ne abu na biyu kuma shine, ina ganin kamar tawa sha’awar  a jinina take domin kuwa iyaye na duka ’yan siyasa ne. Babana ya sha wakiltar jiharmu, san nan kuma mahaifiyata ta yi takara a jam’iyyar ANPP har ta zama kansilan karamar hukumarmu. Mutum ya zama mai gaskiya da taimakon mutane, idan zabe ya zo ba ma sai ka fito ka ce za ka yi takara ba. Mutane ne za su fiddo da kai kuma su zabe ka, don haka a kullum nake jaddada wa mutane da su yi gaskiya da yin adalci a kowane hali suka samu kansu, saboda gaskiya ita ce mai dorewa.
Na iya hulda da jama’a, sai ya kasance a duk lokacin da wani abu ya taso, suke cewa na je na wakilce su, tun da na tashi rayuwata haka ya yi ta faruwa da ni tun daga makaranta firamare har zuwa jami’a. A gaskiya ni mai sauraron koke-koken mutane ne, shi ya sa nake tabbatar da wakilci mutane a kan duk wata damuwarsu, ba sai na fada ba kowa yasan abin da ke faruwa a Jihar Barno, don haka hankali na ba zai taba kwanciya ba har sai mun shawo kan wannan lamarin, takofin yakina ita ce gaskiya, sai idan karfina ya kare.
Ya kike kallon siyasan mata a kasar nan?
Yana da wahala ne abin, saboda maza sun hana mu sakat, muna gwaggwarmayar ci gaba su kuma sai neman su take mu suke, amma yanzu an samu dama-dama, idan aka kwatantan da abin da ya yi ta faruwa a zamanin da kwata-kwata mace ba ta da ta cewa. Musamman a yankinmu na arewa, a da ko makarantar boko ba a barin ’ya mace ta yi, mun gode Allah, don yanzu kam, mun dan samu cigaba, kuma muna nan muna jajircewa don kara samun nasara a rayuwar ’ya mace.
Ko za ki bayyana mana yadda kike ji hada rayuwar aure da wannan aikin?