Dokta Asabe: Maza su ne kalubalenmu(1)

Abu mai mahimmaci da mace za ta fara la’akara da shi, idan har tana so ta yi nasara a harkokin ta na yau da kullum, shi ne ta gina duk wani abu da za ta yi kan yardar mijinta, na biyu ta yi gaskiya, na uku tabbatar da cewa kin tsara rayuwanrki ta hanyar da […]

Dokta Asabe: Maza su ne kalubalenmu(1)
Dokta Asabe: Maza su ne kalubalenmu(1)

Abu mai mahimmaci da mace za ta fara la’akara da shi, idan har tana so ta yi nasara a harkokin ta na yau da kullum, shi ne ta gina duk wani abu da za ta yi kan yardar mijinta, na biyu ta yi gaskiya, na uku tabbatar da cewa kin tsara rayuwanrki ta hanyar da ba za ki samu matsala wurin daidaita gidan ki da kuma aikin ki ba, ko kuma sana’a. Domin rashin yin haka na iya kawo tangarda don haka sai an jajirce sannan za a samu komi na tafiya daidai, shi ya sa ni ba na jin komai hada wadanan abubuwan.
Ko za ki iya gaya mana abin da kika fi so a rayuwa?
Gaskiya da taimakon mutane, wadannan su ne sanadiyar farin cikina. Kuma su ne suka kawo ni wannan matsayin.
Wadanne kalubale, kike fuskanta ta dalilin shigar ki siyasa?
Maza, maza, su ne kalubalen mu, don duk wani abu da za ki yi sai sun nemi su taka su a ganin su, wace ce mace, sannan kuma a halin yanzu da muke ciki shi ne, irin masifun da suka addabi jihohinmu na Arewa-maso-Gabas, duk wani abu da zamu yi ba zai taba burge mutanenmu ba har sai mun shawo kan wannan matsalar.
Ko kina da wani buri? Kuma ya ya kike son a rika tuna ki?
Burina shi ne na ci gaba da taimaka wa yan’uwana mata. Har ila yau, na zama tauraruwar da za a rika koyi da ita. Zan yi aiki nagari da gaskiya iya karfina domin a rika tuna wa da ni kan kyawawan aikina bayan na bar duniya.
Wace shawara gare ki ga mata don gyara rayuwar al’umma?
Shawarata ita ce mu fito kar mu ji tsoro, mu taimaka wa junanmu a duk harkokin zamantakewarmu, kuma mu yi kokarin shiga gwamnati don kare hakkinmu, idan mu manya mun yi haka to, na baya garemu ba za su sha irin wahalar da mu ka sha ba, don samun saukin harkokinmu na yau da kullum da abin gaskiya don ta yadda al’umma nagari. A yanzu ina so ayi dokan cewa a duk wani bangaren shugabancin kasar nan a samu mace guda, wasu wuraren ma fiye da haka. To idan ba mu fito ba, ta ya ya za mu samu wannan ci gaban har mu rika tallafa wa juna.