Dokta Barakat ta bukaci gwamnati ta rika bai wa ’ya’ya mata ilimi kyauta

Shugabar Kwalejin Ilimin kere-kere ta Tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara Dokta Barakat Abubakar ta bukaci fallayen gwamnatociuku, wato tarayya da jihohi da kananan hukumomin kasar nan su maida hankali wajen baiwa ’ya’ya mata ilimi kyauta.Dokta Barakat Abubakar ta bayyana haka ne a yayin da take zantawa da wakilinmu a ofishinta a karshen makon […]

Dokta Barakat ta bukaci gwamnati ta rika bai wa ’ya’ya mata ilimi kyauta
Dokta Barakat ta bukaci gwamnati ta rika bai wa ’ya’ya mata ilimi kyauta

Shugabar Kwalejin Ilimin kere-kere ta Tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara Dokta Barakat Abubakar ta bukaci fallayen gwamnatociuku, wato tarayya da jihohi da kananan hukumomin kasar nan su maida hankali wajen baiwa ’ya’ya mata ilimi kyauta.
Dokta Barakat Abubakar ta bayyana haka ne a yayin da take zantawa da wakilinmu a ofishinta a karshen makon jiya, inda ta ce kiran ya zama wajibi bisa la’akari da tarbiyan yaya mata ta bangaren rashin kulawa wajen sanyasu a makarantu,don samun Ilimin zamani.
Dokta Barakat ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda wasu iyaye saboda talauci suke dora wa ’ya’yansu tallace-tallace don samun kudin shiga maimakon sanya su a makarantun boko.
Ta ce idan gwamnatoci zasu bada fiffikon gaske wajen baiwa ’ya’ya mata ilimi kyauta hakan zai magance tabarbarewar tarbiyyar ’ya’ya mata musamman a Arewa, inda ta ce akwai bukatar a rika wayarwa iyaye kai susan muhimmancin ilimin’ya’ya mata.
Sai ta jinjinawa Gwamnatin Tarayya kan gudunmawar da take bai wa makarantar a fannin gine-ginen ajujuwa da dakunan kwanan dalibai tare da yin kira ga gwamnatin Jihar Zamfara ta kammalaginin da ta fara wanda ya shafi wurin kwanan dalibai a makarantar.