Dokta Fatima Zanna Gana: Komai a yi shi da gaskiya
Dokta Fatima Zanna Gana likita ce,amma daga baya ta bar aikin likita,ta bude makaranta mai zaman kanta.Kuma ta kirkiro cibiya mai zaman kanta mai suna Purple Heart Foundation.Inda take taimaka wa marayu da mabukata.A yanzu haka wannan cibiya tana daya daga cikin wadanda suke taimaka wa mutanen da aka raba su da muhallinsu a jihar […]
Dokta Fatima Zanna Gana likita ce,amma daga baya ta bar aikin likita,ta bude makaranta mai zaman kanta.Kuma ta kirkiro cibiya mai zaman kanta mai suna Purple Heart Foundation.Inda take taimaka wa marayu da mabukata.A yanzu haka wannan cibiya tana daya daga cikin wadanda suke taimaka wa mutanen da aka raba su da muhallinsu a jihar Borno.
Dokta Fatima Zanna Gana an haife ni a jihar Kano inda na fara karatu,amma na kammala ne a makarantar St. Micheals da ke U.K.Daga nan na tafi makarantar sakandare ta Dambo International da ke jihar Kaduna.Na karasa a makarantar Essence International da ke jihar Kaduna. Na yi karatun gaba da sakandare a U.K.Bayan na dawo sai na tafi jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya,ban gama a nan ba sai na tafi jami’ar Maiduguri inda na kammala karatun likita.Na yi aikin likita na tsawon shekara biyu.
Na dakatar da aikina na likita inda na bude makaranta mai zaman kanta kuma na kirkiro cibiya mai zamankanta mai suna Purple Heart Foundation domin taimaka wa marayu da mabukata .Abin da yake damuna shi ne yadda ake ware gidan gajiyayyu daga cikin al’umma,wannan yana bata min rai.Cibiyar tana daya daga cikin wadanda suke taimakawa ’yan gudun hijra a kananan hukumomi 28 da ke jihar Borno.
kalubale
Babban kalubalen da nake fuskanta shi ne rashin kudi.Ina son in yi abin da ya fi wanda nake yi a yanzu,amma abin da kamar wuya ,domin hatta masu ba da tallafi na kasashen waje sukan zabi wadanda za su taimakawa .Amma ba na ganin laifinsu domin akwai mutane da yawa da suke karbar kudi da sunan taimaka wa jama’a,amma sai su cinye kudin ba tare da sun yi abin da ya dace da kudin ba.Wannan halayya ta kawo wa mutane matsala domin hakan ya sa wasu mutane basu da sha’awar taimakawa.Amma ina fata saboda aiyukan da muka yi,mutane za su kawo taimako domin agaza wa mabukata.
Asalin cibiyar Purple Heart
Tun ina ‘yar karama nake da sha’awar taimakon jama’a.Lokacin da muka zauna a Maiduguri,duk lokacin da na ga wani a talabijin yana bukar taimako ta fannin lafiya nakan ba da tawa gudumawar daidai gwargwado.Lokacin muna karatun digiri a jami’a ni da kawayena muna da kungiya mai zaman kanta da muke taimakon marasa lafiya mabukata.Sai dai bayan an kai hari Amerika a watan Satumba 9/11 ,sai muka rusa ta,domin sunan Masulunci ne da ita.
Bayan na yi aure sai mijina ya shawarce ni da in kafa cibiya mai zaman kanta,domin in samu damar yin taimakon sosai.A shekarar 2009 sai na yi tunanin kafa cibiyar Purple Heart.Lokacin muna makarantar sakandire,mun yi rubutu a kan yakin duniya na biyu,a nan ne muka san kyaututtukan Purple Heart da ake bai wa tsofaffin sojojin da suka yi rawar gani.Ina ganin wannan ya yi daidai da halin da muka tsinci kanmu a Maiduguri domin an kashe mu ,an ji mana ciwo kuma babu wanda ya kula mu.Har sai lokacin da ‘yan kungiyar Bring Back Our Girls da saurau kugiyoyi suka fara magana.Da haka ne na kirkiro cibiyar Purple Heart.
Burina ina karama
Lokacin da nake karama ina makarantar firamare ina tunanin gina gidan marayu.Bayan na je makarantar sakandare kuma sai na fara tunanin zama mai zanen gidaje.Amma wata rana ina son ganin likitan mata sai na ce shi likitan ba zai duba ni ba sai dai matarsa,sai ya ce na ki tsayawa ya ganni sai na ce saboda haka nima likita zan zama.Kamar da wasa sai ga shi na karanci fannin likita.
Hada aikin gida da na ofis
Babu sauki ko kadan.daya daga cikin dalilan da ya sa na bar aikin asibiti a wancan lokacin shi ne ba na iya hada aikin gida da na asibiti.Ina da yaro karami kuma ga shi ina zaune a asibiti ina faman aiki abubuwa sun cakude min.Saboda haka zabi ya rage min.Lokacin da na haifi dana na biyu sai na ajjiye aikin,yanzu ina da ‘ya’ya uku.Yanzu tun da ina tsaye da kafafuna na samu damar da zan kula da gidana kuma in kula da harkokin kasuwancina yadda ya kamata.Mijina mai fahimta ne sosai,don haka wannan ya taimaka wajen kawo saukin al’amura da ci gaba.
Lokacin da na zama uwa
Lokacin da na haifi dana na fari sai nake ganin duk wanda ya dauke shi zai je ya ajjiye shi ne.Na yi mamaki matuka lokacin da na haife shi,ba zan iya bayyana yadda nake sonsa a cikin zuciyata ba.Kowa yana magana a kan soyayya,amma mutum bai santa ba har sai ya dauki dansa a hannunsa tukuna.
Abin da ba na mantawa
Lokacin ina karama,ina ganin komai yana ba ni sha’awa.domin Babana mai sha’awar tafiye-tafiye ne.Ba sai mun fita kasar waje muke shakatawa ba.Lokacin akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali.Da zarar mun dawo daga makaranta za mu tarar an zuba mana kayanmu a bayan mota an yi shirin tafiya.Ko dai Yankari ko wanai wuri a Najeriya.Wannan abu yana faranta min rai.
Mutanen da nake koyi da su
Zan iya cewa iyayena da surukaina,musamman uban mijina.Domin mutum ne mai saukin kai sosai.Uwar mijina kuwa da mahaifiyata kusan halinsu iri daya ne.Mutane ne masu rikon addini,har addu’a nake yi domin in zama kamar su.Maganar gaskiya kuwa na shaku da mahaifina matuka.Babu abin da zan iya boye masa a duniya,yana da kulawa sosai.Ta bangaren mijina kuwa,ba miji ne kawai a gare ni ba, babban,abokina ne.Kuma yana ba ni matukar goyon baya a kan duk abin da na sa a gaba.
Darasin da na koya a rayuwa
Abin da na koya a rayuwa shi ne, yi wa mutane uzuri.Kuma kada ka zaci don ka taimaki mutum shi ma zai taimaka maka.Na fahimci kada ka rabu da kawayenka na yarita komai tsanani, domin su ne kawaye na gaskiya.Sannan kuma kada ka watsar da ‘yan uwanka.ko me ka mallaka a duniya.
Abin da na koya a rayuwar aure
Kada mutum ya rika boye-boye,ban taba boye wa mijina wani abu ba ko sau daya,tun ma kafin mu yi aure.Ni tsarina shi ne komai a yi shi da gaskiya .Idan akwai matsala sai mu hadu mu gyara da kanmu.
Yadda na hadu da maigidana
Na san ‘yar uwasa da mahaifiyarsu tun kafin na hadu da shi. kanwarsa tana gaba da ni a makarantar Essance. Mun san juna a matsayinmu na Kanuri a can.Mun kara shakuwa ne lokacin da zan yi rubutu a kan Leaonard Da binci,sai aka ce min akwai wata daga Borno da take irin wannan rubutu za ta iya taimaka min.Sai na ga ashe Fanna ce daga ranar muka kulla zumunta sosai.
Yunus,wato mijina shi ne na karshe da na hadu da shi a danginsu lokacin yana Maiduguri yana aikin PTF.Shekara daya kafin mu hadu,lokacin watan Ramadan mahaifiyata ta ce na dace da shi.Sai na yi fushi da ita.Abin mamaki bayan kamar shekara hudu sai ya kasance mijina.Fatan da mahaifiyata ta yi a lokacin Ramadan ya zama gaskiya.
Abin da na fi so tare da shi
Abin da nake so game da mijina ,shi ne kamun kai.Kuma ina ganinsa kamar mahaifinsa.Domin mahaifansa suna jin dadin rayuwarsu da ‘ya’yansu da jikokinsu.Don haka ni ma ina fatan Allah ya ba mu tsawon rai da kuma zaman lafiya.
Kwalliya
Akwai matan da ba sa iya zama ba tare da kwalliya ba.Amma ni yawanci idan za mu je sha’ani musamman da mijina nakan yi kokari in ga na yi kyau.
Abin da nake so a tuna ni da shi
Ina so a tuna ni a matsyin wadda ta taimaka wa al’ummarta sosai.Kuma ina so makaranta ta ci gaba har bayan raina.Domin na tabbata wannan shi ne babban abin da za a tuna ni da shi.