Dokta Hassan Dikko ya bukaci al’ummar Jos su rika gyara hanyoyinsu da kansu

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Filato, Dokta Hassan Abubakar Dikko ya shawarci al’ummar garin Jos su tashi su gyara hanyoyin unguwannan da suke zaune da kansu. Dokta Hassan Dikko ya yi wannan kira ne a lokacin da yake jawabi wurin rufe musabakar reshen kungiyar karo na 18 […]

Dokta Hassan Dikko ya bukaci al’ummar Jos su rika gyara hanyoyinsu da kansu
Dokta Hassan Dikko ya bukaci al’ummar Jos su rika gyara hanyoyinsu da kansu

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Filato, Dokta Hassan Abubakar Dikko ya shawarci al’ummar garin Jos su tashi su gyara hanyoyin unguwannan da suke zaune da kansu.
Dokta Hassan Dikko ya yi wannan kira ne a lokacin da yake jawabi wurin rufe musabakar reshen kungiyar karo na 18 da aka gudanar a Jos.
Ya ce “Mu mutanen Jos mu tashi mu gyara hanyoyin unguwannin da muke zaune da kanmu, musamman ganin yadda gwamnati ta yi watsi da mu, ta ki gyara mana. Muna ganin yadda ake yin hanyoyi a jihar nan a wasu wurare, amma babu motocin da suke bin hanyoyin, amma a nan garin Jos, inda miliyoyin mutane suke zaune hanyoyinsu duk a lalace an ki a gyara.”
Don haka sai ya bukaci masu hali su taimaka wajen gyara hanyoyin inda ya ce, “Wannan aiki bai fi karfinmu ba, amma saboda mutuwar zuciya ta hana mu gyara hanyoyin namu, a lungunan unguwanninmu za ka samu gidan Naira miliyan 30, amma saboda son dukiya mai wannan gida ya kasa taimakawa a gyara hanyar da zai bi zuwa gidan.”
Dokta Dikko ya ce inda mutum yake zaune nan ne mutuncinsa yake. “Gyara hanyoyinmu ni’imarmu ne da mutuncinmu baki daya,” inji shi.
’Yan takara 108 da suka fito daga kananan hukumomin jihar ne suka fafata, kuma Adam Ibrahim Adam daga karamar Hukumar Kanam ne ya zama gwarzon shekara, inda ya samu kyautar Keke NAPEP, yayin da sauran wadanda suka samu nasara a sauran matakai suka samu kyaututtukan kekunan dinki da firiji da akwatunan talabijin da sauransu.